
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jam’iyyar adawa ta NDC ta tabbatar da Peter Obi a matsayin ɗan siyasa ɗaya da yanki tikitin takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashinta.
Hakan na zuwa ne bayan da sauran masu neman takarar suka janye ko kuma suka gaza cika wasu daga cikin sharuddan da aka gindaya.
Wannan ci-gaba ya ba Obi damar zama babban ɗan takarar da jam’iyyar za ta dogara da shi wajen fuskantar babban zaɓen da ke tafe.
Tuni dai magoya bayan jam’iyyar suka fara nuna farin ciki da wannan mataki, suna masu bayyana cewa hakan zai taimaka wajen ƙarfafa haɗin kai da kuma tsara yakin neman zaɓe cikin tsari.
Masana harkokin siyasa na ganin cewa wannan dama za ta bai wa Obi cikakken lokaci da nutsuwa wajen bayyana manufofinsa ga al’umma musamman akan batutuwan tattalin arziƙi, tsaro da inganta rayuwar jama’a.
Saidai, wasu na ganin cewa kasancewarsa shi kaɗai a takarar na nufin babban nauyi ya rataya a kansa, domin yanzu hankalin jam’iyya da na al’umma gaba ɗaya za su karkata gare shi wajen ganin irin rawar da zai taka.
