APC ta yi amai ta lashe bayan ayyana Yusuf Gagdi a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen fidda gwani

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jam’ian jam’iyyar APC sun gyara kuskurensu na zaɓen fidda gwani, inda suka ce Yusuf Gagdi ne ya ya yi nasara a takarar Majalisar Wakila.

Hakan na nufin kwamitin zaɓen na APC a Jihar Filato ya yi amai ya lashe akan nasarar Yusuf Gagdi, wato ɗan majalisa mai wakiltar Pankshin/Kanke/Kanam.

An sanar da haka ne a Sakatariyar APC da ke garin Jos daga Shugabar kwamitin zaɓen fidda gwanin, Stella Okotete, wadda ta ce sanarwar farko an yi ta ba tare da izini ba don haka ba karɓaɓɓiya ba ce.

Okotete ta bayyana cewa babban baturen zaɓen ne kaɗai aka ba izinin sanar da sakamakon zaɓe, tana mai cewa duk wata sanarwa da aka yi saɓanin haka abin a yi watsi da ita ne.

Ta ƙara da cewa, babban baturen zaɓen shine, Nandom Kura, wanda a yanzu ya ayyana Gagdi a matsayin sahihin wanda ya lashe zaɓen na ranar Asabar.

By Babaji