2027: SERAP ta buƙaci INEC ta bayyana adadin kuɗaɗen da doka ta ƙayyade wa jam’iyyu su kashe yayin yaƙin neman zaɓe

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja.

Cibiyar kula da ‘yancin zamantakewa da tabbatar da gaskiya da adalci a Nijeriya (SERAP), ta yi kira ga Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, da ya yi amfani da ikon da dokar ƙasa ta bayar wajen bayyana ainihin adadin gudunmawar da ta halasta a bayar a harkokin siyasa ƙarƙashin Sashe na 91 na Dokar Zaɓe ta 2026.

Haka kuma, SERAP ta roƙi hukumar da ta wallafa ainihin adadin da aka ƙayyade da kuma sanar da su ga jam’iyyun siyasa, ‘yan takara, masu taimakawa da kuma al’ummar ƙasa domin tabbatar da biyayya ga hukunce-hukuncen sashen.

Ƙungiyar ta yi wannan magiya ne a wata takarda da ta yi wa laƙabi da Buƙatar ‘Yancin samun Labari, wadda ta fitar a ranar Asabar ta hannun Maitaimakin Daraktanta, Kolawole Oluwadare. Sannan SERAP ta nemi INEC da ta bayyana tsare-tsare da hanyoyin da ta samar da sanya ido, bincike da tabbatar da biyayya ga gudunmawar siyasa da ƙayyadaddun adadin kuɗaɗen yaƙin neman zaɓen yayin tunkarar 2027.

Ta buƙaci hukumar zaɓe da ta bayyana salon hanyarta na sanya ido kan kuɗaɗen zaɓe, ciki har da gano tsare-tsaren ganowa da warware matsalolin gudunmawar da aka samu na tsabar kuɗi da waɗanda aka tura ta asusun bankuna ta yadda za a tabbatar da haƙiƙanin yadda al’amarin ya gudana.

Kazalika, SERAP ta ce ainihin gaskiya da adalci a samar wa siyasa kuɗaɗe na da muhimmanci wajen tabbatar da gudanar da zaɓuka bisa tsarin doka ta yadda al’umma za su zaɓi ra’ayinsu ba tare da an sauya musu tunani ba da kuɗaɗe ko wasu ababen alfarma.

Wannan na zuwa ne ƙasa da mako guda da INEC ta kaɗa gangar siyasa yayin tunkarar babban zaɓen 2027, inda tuni ‘yan takara a matakai daban-daban suak fara yaƙin neman zaɓensu.

By Babaji

Leave a Reply