2027: Shugaban matasan ADC ya yi murabus sa’o’i bayan Atiku ya fitar da kwamitin yaƙin neman zaɓensa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaban matasan jam’iyyar ADC, Sultan Bello, ya yi murabus daga jam’iyyar.

Bello ya sanar da wannan mataki ne a wata takarda mai ɗauke da 24 ga Satumba, 2026, wadda ya aike wa Shugaban jam’iyyar na Gundumar Gyaɗi-Gyaɗi da ke Ƙaramar Hukumar Tarauni, inda ya ce ya ɗauki matakin ne bayan shawarwari da dogon nazari da kuma raɗin kai.

Ya kuma ce, wannan mataki ya fara aiki ne a nan take yayin da yake shirin sauya akalar siyasarsa, yana mai godiya ga jam’iyyar bisa damar da ta ba shi na yi mata hidima sakamakon amincewa da shi.

Sultan Bello, ya kuma yi godiya ga Mai Girma Rt. Hon. Rotimi Amaechi bisa shawarwarinsa a gare shi, yarda da goyon bayansa wajen yin aiki tare da shi, inda ya bayyana godiyarsa tare da masa fatan alheri a harkokinsa na nan gaba.

Kazalika, ya miƙa godiyarsa ga jagorancin jam’iyyar, masu ruwa da tsaki, mambobi da magoya bayanta bisa damar da ya samu na hidima da bayar da gudunmawarsa ga jam’iyyar.

By Babaji

Leave a Reply