2027: Yari ya yi jawabi karon farko a matsayin darakta-janar na yaƙin neman zaɓen Tinubu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kafa kwamitin yaƙin neman zaɓensa a babban zaɓen 2027, Darakta-Janar na tafiyarsa a jam’iyyar APC, Sanata Abdulaziz Yari Abubakar, ya karɓi muƙamin a hukumance inda ya ci alwashin sauke nauyin da aka ɗora bisa jajircewa da ladabi wajen kai su ga nasara a 2027.

An zaɓi Yari, wanda shi ke wakiltar Zamfara ta Yamma a Majalisar Dattawan Nijeriya kuma tsohon Gwamnan Jihar Zamfara ne a matsayin Darakta Janar na yaƙin neman zaɓen Tinubu a ranar Asabar, 22 ga Agusta.

A wata sanarwa da sanatan ya fitar a Abuja, ya yi godiya ga Shugaba Tinubu da jagorancin APC bisa amanna da shi, yana mai cewa a shirye yake ya sauke nauyin da aka ɗora masa.

“Na karɓi wannan nauyi da hannu biyu-biyu da cikakken yaƙinin saukewa. Godiyata mara adadi ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar bisa ƙwarin-gwiwarsu a kaina, da jagorancin jam’iyyarmu bisa amanna da ni. Ba zan yi sako-sako da shi ba,” inji Yari.

Wannan jawabi na zuwa ne jim-kaɗan bayan kafa kwamitin tsare-tsaren yaƙin neman zaɓe domin zaɓen 2027 wanda Tinubu ne shugabansa, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima a matsayin maitaimaki da Shugaban APC na Ƙasa a matsayin mataimaki na biyu.

A cewar Yari, yaƙin neman zaɓen zai bai wa APC damar damawa da ‘yan Nijeriya daga sassa daban-daban na ƙasar da gabatar da hange mai kyau ga goben ƙasa, yana mai cewa za su tabbatar da an gudanar da yaƙin neman zaɓen bisa ladabi da haɗin kai tare da mutunta ‘yan ƙasa ba tare da la’akari da bambamce-bambancen jam’iyya ba.

By Babaji

Leave a Reply