Daga WAKILINMU
Nijeriya ta tura gudunmawar ‘yan sanda su 144 ya zuwa ƙasar Somaliya domin aikin tallafa wa fannin tsaron ƙasar.
Nijeriya ta tura jami’an nata ne ƙarƙashin tawagar AMISOM ta ƙungiyar tarayyar Afirka (AU).
Babban jami’in tsare-tsare na tawagar AMISOM a ƙasar, Daniel Ali Gwambal, ya bayyana cewa 30 daga cikin ‘yan sandan za su yi aiki na tsawon shekara guda ƙarƙashin tawagar AMISOM, inda za a tura su yankunan Beletweyne da ke jihar HirShabelle, sauran kuma za su yi aiki a sassan birnin Mogadishu babban birnin ƙasar.
Jami’in ya ce sauran ‘yan sandan za su yi ayyukan tsaro da bada kariya ga manyan jami’ai da bada horo da tallafa wa ‘yan sandan ƙasar wajen wanzar da zaman lafiya.
Haka nan, ya ce za kuma su riƙa shiga ayyukan sintiri tare da takwarorinsu na Somaliya, domin ba da kariya ga muhimman cibiyoyin gwamnati da wuraren taruwar jama’a.
CRI ta ruwaito tawagar AU na fatan zuwan ‘yan sandan Nijeriya ƙasar Somaliya, zai taimaka wajen bunƙasa ayyukan kiyaye doka da oda duba da za su yi aiki tare da ‘yan sandan
ƙasar wajen tabbatar da an inganta tsaro a ‘yantattun yankunan ƙasar.
