Daga AMINA YUSUF ALI
A yanzu haka dai masu kamfanonin buga ruwan leda (fiyawota) a Abuja sun ba da sanarwar ƙarin farashin ruwan leda (fiya wata/ pure water) a faɗin birnin na Abuja. Inda suka bayyana cewa za su fara bayar da sarin kowacce leda a kan Naira 200 inda su kuma masu sayar da ɗai-ɗai za su dinga sayar da shi a kan Naira 240 duk leda ɗaya, kuma idan ƙwalli ɗaya ne, Naira ashirin kowanne ɗaya.
Masu kamfanonin ruwa sun bayyana cewa, farashin ruwan ya ƙaru ne sakamakon ƙaruwar farashin kayan aikin da suke amfani da su a kasuwa. Saboda halin karayar arziki da ƙasar Najeriya ta samu kanta a halin yanzu.
Sakamakon rashin samun tsaftataccen ruwan sha a ƙasar, miliyoyin ‘yan Nijeriya sun dogara ne kacokan a kan ruwan leda na fiya wata don kashe ƙishinsu. Inda yanzu kuma farashinsa ya yi tashin gwauron zabi ya ninka farashinsa ya koma Naira 20 ba kamar yadda ake sayar da shi a kan Naira 10 ba a baya.
Masu kamfanonin buga ruwa daga ƙungiyar buga ruwan (ATWAP) sun ce ba yadda suka iya ne da tsadar abubuwa. Su ma dole ce ta sa suka ƙara farashin ruwan saboda tsadar kayan aikin buga ruwan.
Shi ma shugaban ƙungiyar masu kamfanonin buga ruwa (ATWAP) reshen Birnin Tarayya Abuja, Mohammed Akwuh, ya tabbatar da wannan labari. Inda ya kara da cewa, farashin ruwa a da ba ya wuce Naira 120 zuwa Naira 150 farashin sari a kan kowacce leda.
Ya bayyana cewa, farashin ya ƙaru ne sakamakon ƙarin farashin kayan aikin nasu. Abin ba daga su ba ne, a cewarsa. Kuma a cewar sa abin ba su kaɗai ya shafa ba. Don ko makwabtansu jihohin Neja da jihar Nasarawa sun yi ƙarin farashin sayar da ruwan shan tun a watan Agustan da ya gabata.
