E-Naira: Kamfani ya maka CBN a kotu kan zargin satar fasaha

Daga AMINA YUSUF ALI

A halin dai da ake ciki, kotu ta aike wa da Babban Bankin Najeriya CBN, takardar sammaci, a kan zargin satar fasaha da wani kamfani ya yi ƙarar CBN ɗin a kai. Kamfanin ya zargi CBN da yi masa wankiyar fasaha inda ya ce shi ya fara ƙirƙirar fasahar e-Naira. Inda ya nemi kotu ta tursasa Bankin ya cire sannan ya canza wannan sunan na e-Naira domin haƙƙin mallakar kamfaninsa ne.

Waɗannan bayanai suna ƙunshe ne a cikin takardar da kamfanin ya aike wa kotu wacce ta ƙunshi sa hannun Olakule Agbebi Esq a madadin kamfanin Olakule Agbebi & Co., inda kamfanin ya ke zargin CBN da satar mu su sunan kamfani.

 Wannan sammaci dai ya biyo bayan sanarwar da babban Bankin ya yi a kwana-kwanan na a kan ya kammala shirye-shiryensa na bu]e zauren yanar gizo inda za a fara hada-hadar Naira ta yanar gizo wacce ya ba wa suna da e-Naira.

A cewar lauyan masu ƙarar, satar fasahar sunan kamfanin da aka yi masa ne, na ‘e-Naira solutions’ ya sa wanda yake ƙarar  ya garzaya babbar kotun Abuja domin shigar da ƙara mai lamba: FHC/AB/CS/113/202. Domin a bi masa haƙƙinsa kuma a hana baban Bankin ƙaddamar da shirin e-Naira ranar 1 ga watan Oktobar nan da ta gabata kamar yadda Bankin ya alƙawarta.

Wataƙila ma wannan yana daga cikin dalilan da Babban Bankin ya ɗage ƙaddamar da e-Naira ɗin a ranar da ya fara sanarwar zai ƙaddamar.