BIDIYO: Buhari ya bayyana dalilin rashin zuwansa Zamfara

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana dalili da kuma rashin jin daɗinsa dangane da zuwa Zamfara da bai yi ba a ranar Alhamis.

Tun farko, an shirya ne a kan Buhari zai ziyarci Jihar Sakkwato sannan ya ƙarasa Jihar Zamfara duk a rana guda, amma daga bisani sai ya taƙaita ziyarar tasa a Sakkwato kawai sannan ya juya ya koma Abuja.