Matsalar tsaro: Laifin gwamnati ko na al’umma? (2)

Daga NAFI’U SALISU

A makon da ya gabata mun kawo muku irin gudunmowar da al’umma suke bayarwa wajen haifar da rashin tsaro. Sannan mun fara kawo muku gudunmowar da gwamnatin Nijeriya ita ma take yi wajen kawo rashin tsaro. Inda muka tsaya a inda za a lasafto hanyoyin da gwamnati take ba da gudunmowa wajen samar da rashin tsaro. A sha karatu lafiya. 

Cin hanci da rashawa:
Aikata cin hanci da rashawa, wani babban al’amari ne da ya taka mummunan rawa wajen lalacewar al’amuran tsaro a ƙasar nan. Domin idan muka kalli jami’an tsaronmu a da, za mu ga mutane ne masu tsayawa a kan dokar ƙasa da kyautata ayyukansu. Mu fara ta kan jami’an ‘Yansanda. ‘Yansanda su ne ajin farko da suka  taka rawa wajen lalacewar mutane a fannin taɓarɓarewa tsaro da kuma aikata miyagun laifuffuka daban-daban. Domin ɗansanda a Nijeriya zai kama mai laifi da hannunsa, amma da zarar an nuna masa kuɗi, sai ya saki mai laifi. Haka nan Alƙalai sun ba da gudunmawarsu wajen lalacewar al’umma, domin ƙiri-ƙiri Alƙali zai juya gaskiya ta koma ƙarya. Ko da ya fahimci cewa lauya da ke ƙoƙarin kare masu laifi ba ya gabatar da shaidu ingantattu don kare marasa gaskiya.

Ko kuma idan aka zagayo ta bayan fage aka nuna masa kuɗi, sai ya yanke hukunci tare da nuna cewa, shaidun da aka gabatar (na ƙarya) an gamsu da su. Don haka sai a yanke hukuncin zalunci a kan mai gaskiya a ɗora masa sharri, wanda hakan shima ta’addanci ne. Don haka, da zarar wancan mutumin mai gaskiya ya gano cewa an yi amfani da kuɗi ne wajen canza ƙarya ta koma gaskiya, to shi ma duk lokacin da ya samu dama, haka zai yi. Ya yi laifi a kama shi, ya ba da kuɗi, a ƙyale shi. 

Idan mun dawo kan batun ‘Yansanda, za ka ga attajiri ko ɗan gidan attajiri ya yi kisan kai da gangan, amma da haɗin bakin ɗansanda, sai ka ga an tura ɗan mai kuɗin zuwa ƙasar waje. Sai a shigar da rahoton cewa, ya tsere. Wani lokacin ma sai a yi maryar an kama shi an tsare, ko kuma an kashe shi. Amma a baɗini yana ƙasar Turai yana holewarsa an ba shi maɓoya. Ko kuma ɗan attajiri ya ɗauko mota ya fito titi yana gudun wuce sa’a, har ya kasance haɗari ya afku a dalilin ganganci da mugun gudun da yake yi da mota ko mashin. Kuma ya kaɗe wani ko wasu ya ji musu rauni. Da zarar an kama shi ya buga waya, sai ka ga mahaifinsa ya kira Shugaban ‘yansanda, nan take sai a saki yaronsa. Shi ya sa za ka ga wasu daga cikin Attajirai da ‘yan siyasa ba sa girmama ɗansanda a ƙasar nan. Domin ko a titi sukan zubar da ƙimarsu da martabar aikinsu (koda suna cikin kaki), ta hanyar kwantar da kai cikin ƙasƙanci ga masu hannu da shuni, ko ‘yan siyasa da masu mulki.

Rashin ba wa al’umma ingantaccen ilimi:
Sannan Gwamnati ba ta samar da ingantaccen ilimi ga ‘yan ƙasa ba, wanda shi ma wannan wani nau’i ne mai ƙarfin gaske da ya taka muhimmiyar rawa wajen rashin samun tsaro. Dalili kuwa shi ne, idan da Gwamnati ta samar da ingantaccen ilimi ga ‘yan qasa, ya kasance a ce ɗan ƙasa zai yi karatu ko iyayensa suna da kuɗi ko ba su da shi (kamar yadda su manyan ƙasar suka yi karatun a sadaka a can baya). To da ba a samu yawaitar ayyukan ta’addanci a ƙasar ba. Domin shi ilimi yana gyara zukatan al’umma, yana haska musu zuciya. Kuma da ilimi ne ake tausar zuciya.

A maimakon haka, sai mahukunta suka kyautata rayuwar ‘ya’yansu, suka ba su ilimi mai kyau. Makarantar ‘ya’yansu ta kuɗi ce ba ta Gwamnati ba. Haka nan asibitocin da ‘ya’yansu suke zuwa ana duba lafiyarsu ba ɗaya ba ne da asibitocin da talakawa suke zuwa. Sannan iyalansu a killace suke. Wasu ma ‘yan siyasar da masu riƙe da madafun iko, matansu ko a hoto ba za ka gansu ba ballantana a fili. Don haka, duk lokacin da za ka ji ana neman taimakon kuɗin jarrabawa a gidajen rediyo da talabijin, to za ka samu ‘ya’yan talakawa ne suke neman wannan taimakon. Kuma sai hakan ya zamo tamkar kasuwa, idan ya nema ya samu, sai wani ma ya ɓullo. Haka nan ‘ya’yansu suna cin jarabawa ko ta halin ƙa-ƙa, amma ‘ya’yan talakawa sai sun yi kamar za su yi hauka, abin da masu iya magana suke kira da; ‘da ƙyar na sha’

Ɓangaren ababen more rayuwa
Akwai abubuwan more rayuwa irin su; ruwan sha, wutar lantarki, hanyoyi, tsaro, kiwon lafiya, sana’o’i, Ayyukan yi da dai sauransu. Duk a zahiri waɗannan abubuwan akwai su. Amma a baɗini babu su a ƙasa. ‘Yan ƙasa ba sa cin moriyar ayyukan raya ƙasa. Sai dai a yi wasu abubuwa ‘yan kaɗan. Su ma kuma sai lokacin neman ƙuri’a ake aiwatar da su, ba don komai ba sai don a ja hankulan mutane su zaɓi wanda a ke son a zaɓa.

Akwai tarin alƙawurra da ‘yan siyasa suke yi wa al’umma kafin su ci zave, alƙawuran gina rayuwar al’umma da bunƙasa su, to amma da zarar burinsu ya cika, sai dai ka riƙa ganin fuskokinsu a jaridu da mujallu, ko ka ji muryarsu a kafafen yaɗa labarai. Sannan tafiye-tafiye marasa kan-gado kuwa ba a magana. Sun yarda su ɓata lokacinsu a tafiye-tafiyen yawo hutu da buɗe ido, amma ba su da lokacin da za su riqa zagayawa cikin al’umma don sauraren koken mutane, ko sa ji damuwarsu, su share musu hawaye. 

To kuma wannan shi ne aikin duk wani shugaba, matuƙar shugaba ba shi da lokacin da zai saurari buƙatun al’ummarsa, to me ya rage masa a shugabanci face ya sauka kurum, tunda ba shi da lokacin sauraren mutanen da yake mulka? Tunaninsa ba a kansu yake ba, idan ka ga yana ƙoƙarin waiwayonsu, to lokacin zaɓe ne ya sake tahowa. Sai ka gan shi gari-gari, unguwa-unguwa, saƙo-saƙo. Ko hanyar ƙauye ce mai kwazazzabai da ramuka gami da ƙayoyi zai shiga Jif ya tafi. Wani lokacin har da takawa a ƙafa ya isa cikin talakawa.

Amma da zarar buƙatarsa ta biya, to sai dai ka ga hotonsa a jikin bango, tun wanda a ka liƙa lokacin da ya zo neman ƙuri’a.
Don haka masu mulkinmu ba su shirya gyaran ƙasa ko inganta ‘yan ƙasa ba. Abinda suka fi mai da hankali kawai shi ne, ɓallo abubuwa rututu da nufin ayyukan raya ƙasa a zahiri, amma a baɗini, ayyukan kashe mu raba ne don samun (Percentage) wato wani kaso a cikin kuɗin ayyukan. Kuma sai ka ga wasu ayyukan da yawa ba a haɗa su har Gwamnatin ta ƙare, wata ta zo. 

Na taɓa jin wani mai mulki suna maganar sirri shi da wani mataimakinsa, yayin da mataimakin nasa ke sanar da shi koken al’umma, tare da ankarar da shi ya kamata a sauke nauyin al’umma. To amma abin mamaki shi wannan shugaban sai yake nuna wa mataimakinsa cewa, “A lokacin da ake kan mulki ba a tunanin al’umma…” to tunanin me ya kamata a yi kenan? A tawa tambayar. To kun ga kenan masu mulki ba ta al’ummar da suke mulka suke yi ba, domin kuwa da ta tasu suke yi, da duk wata hanyar da za a rasa rai za su daƙile ta.
An sha gani a jaridu da kafafen yaɗa labarai, a wasu ƙasashen waje shugabanni kan yi murabus a kan wani abun da idan mu a nan ƙasar ne, ko gezau shugaba ba zai ji a zuciyarsa ba. Domin ga misali nan a bayyane muna gani.

An kashe bayin Allah a ƙasar nan, ana ci gaba da kashewa. Ayyukan garkuwa da mutane, fashi da makami, sata, damfara, ayyukan fyaɗe, sace kuɗin ƙasa, cin hanci da rashawa. Duk sun yi yawan da lissafinsu hankali ba zai iya ɗauka ba idan aka ba da ƙididdiga. An dakatar da al’amura da dama a ƙasar nan wanda talaka yake yi don samun abin kai wa baki, amma ko sau ɗaya ba su taɓa daina tarukansu na siyasa ba. Ana kashe jama’a a can, su kuma suna taron siyasa a nan. Ana ƙone-ƙone da sace-sacen al’umma, da rashin kyan hanya, da kwashe mutane a kan hanya a tafi daji da su, a nemi kuɗin fansa, da fashi da makami cikin gari, amma duk wannan ba ya daga cikin abinda yake hana su barci saboda tunanin ya za su magance. Amma a kan yaya za su maimaita hawa kujerar mulki, har umarnin harbi ake bayarwa ga duk wanda ya saci akwatin zaɓe. 

Rashin adalci da haifar da tarzoma
Akwai abubuwan da suka zamo na rashin adalci da ake yi wa ‘yan ƙasa. Wanda wannan yana tunzura wasu daga cikin ‘yan ƙasa su canza ra’ayinsu kyakkyawa na kishin ƙasa da son ci gabanta, su koma ‘yan ta’adda. Misali; an yi maka rashin adalci (ba a baka haƙƙinka ba) ka fito ka yi magana ta inda za a gani (kafar yaɗa labarai ko zanga-zangar lumana), sai a bi ka a kama ka. Sannan za ka sha wahala kana kasuwanci, ba ka da hanya mai kyau da ka ke yin sufuri, ga kuɗin haraji mai yawa, ga rashin tsaro da yake haifar da fargabar fita daga gida, ko zuwa cin kasuwa, kai ziyara wani gari da sauransu. Ko kaɗan ba ka ji a ranka cewa za ka isa inda ka nufa lafiya ba. Ka biyo hanyar da ake garkuwa da mutane ko a harbe, amma da ka samu inda jami’an tsaro suke, sai ka ga suna neman wani abu a gurinka, idan ba ka bayar ba kuma su yi maka wulaƙanci. Gwamnati kuma ta san da wannan amma ba ta hana jami’in tsaro ya ci zarafin farar hula ba, me zai sa mutane ba za su sauya tunani ba?  Tunanin ɗaukar makami su yi ta’addanci. Haka nan talakawan ƙasa ba su damu da me Gwamnati ke samu, da me take kashewa a ƙasa ba. Amma duk da haka, sai an yi wa talaka bi-ta-da-ƙulli.
Shi ya sa ake yi wa Gwamnati kallon tana da wata ajanda da wasu gurɓatattun mutane da suke da mummunar manufa wajen samar da rashin zaman lafiya. Ba don komai ba sai don sun wawashe dukiyar ƙasa. Domin shi talaka ko ana zaman lafiya babu ruwansa da abin da Gwamnati ke samu ko wanda take ikirarin tana yi wa ‘yan ƙasa ayyuka. To ballantana kuma a ce babu rashin zaman lafiya. Shi ya sa irin ƙasashen da shugabanninsu suka kasance makwaɗaita, sai su ƙirƙiri abubuwan ta’addanci su wanzar da su, a yi ta tashe-tashen hankula cikin ƙasa, su kuma suna gefe suna sace dukiyar ƙasa suna ɓoyewa. Ƙasashen da ake ganin za su sa ido a yi maganin abin, su ma sai ka ji sun yi gum da bakunansu. Sai wani lokaci ka ji sun yi magana cikin kakkausan harshe kamar da gaske, amma daga nan sai ka ji shiru wai Malam ya ci Shirwa.

Da wannan na ke kira ga shugabanni cewa lallai su ji tsoron Allah, su sani cewa, duk wani shugaba sai Allah Ya tsaida shi a gabanSa ya tambaye shi game da mulkinsa. Don haka, ya kamata shugabanni ku yi kishin al’umma da ƙasa bakiɗaya cikin tausayawa da kuma jin tsoron Allah.

Nafiu Salisu, Marubuci/Manazarci; [email protected], [email protected], 08038981211

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *