Matsalar watsi da gine-ginen da ba a kammala ba

Watsi da gine-ginen da ba a kammala ba, ya zama ruwan-dare a jihohin wannan ƙasa da ma Babban Birnin Tarayya, Abuja. Ko shakka babu, wannan wata gazawa ce ko abin kaico ga wannan ƙasa tamu baki ɗaya. A wani bincike na kwana-kwanan nan, ya bayyana kimanin sama da gine-gine 665 da aka gaza kammalawa a Abuja, da ya haɗa da gidajen zama da kuma na kasuwanci. Abu ne mai sauƙi ka ga an yi watsi da katafaren gida na Milyoyin kuɗi a Abuja.

Haka nan, baya ga rashin kyan gani da waɗannan gine-gine da aka yi watsi da su ke da shi, yana kuma zama barazana musamman ta ɓangaren tsaro ga waɗanda ke makwabtaka da su, ta hanyar zama wata mafaka ta masu aikata laifuka ko ’yan ta’adda da ke laɓewa suna cin karensu babu babbaka a ciki. Koda yake, wasu na ganin cewa matsalar watsi da gine-ginen da ba a kammala ba, ko dai rashin tsari ne na masu mallakin wurin ko kuma kawai rashin ko-in-kula ne irin na masu hannu da shuni, musamman waɗanda suka wawashi dukiyar al’umma da ba za su iya kaiwa banki ko gida su ɓoye ba. Saboda haka, ko ma dai mene ne, wannan ya saɓa da tsarin da gwamnati ta tanadar akan harkar da ta shafi gidajen zama da na kasuwanci don amfanin al’ummarta.

Waɗannan gidaje na nan da dama a cikin birane da wajensu da aka yi watsi da su. Wasu almajirai da nakasassu ne ke kwana a ciki, wasu kuma masu ƙaramin ƙarfi waɗanda ba za su iya kama haya ba ne suka samu suka maƙale a ciki, ganin cewa babu wani wanda zai zo ya daga musu hankali ko ya bigi ƙirji ya ce da su nasa ne. A wasu lokutan, irin waɗannan gine-gine kan rushe har su yi sanadiyyar rasa rayukan wasu da ba su ji ba, ba su gani ba. Haka kuma, wasu daga cikin irin waɗannan gine-gine da aka yi watsi da su, gwamnati ce da kanta ta kwace daga hannun wasu ta kuma musanya musu da wasu amma ta yi watsi da su.

Har ila yau, ɗaukar tsawon lokaci ana Shari’a Kotu a kan matsalar ire-iren waɗannan gidaje, shi ma na taimakawa wajen matsalar watsi da irin waɗannan gine-gine, yana kuma kawo tsaiko wajen kammala su. Bugu da ƙari, abin haushi da takaici, bincike ya nuna mafiya yawan waɗannan gine-gine da ba a kammala ba, mallakar gwamnati ne. Amma saboda yanayi na cin hanci da rashawa da ke kewaye da gwamnatoci, yasa kacokan ba ma a tunawa da su ko ba su muhimmanci ballantana a kai ga kammala su, an fi so a bar su kullum kuɗinsu na sake hauhawa. Don haka, Blueprint Manhaja ba ta ware kowa ba, daga kan gwamnati zuwa sauran ɗaiɗaikun mutane da suka mallaki waɗannan gidaje, ya zama wajibi Hukumar wannan ƙasa ta yi doka ta magance matsalolin watsi da irin waɗannan gine-gine da aka yi watsi da su.

Kazalika, a baiwa waɗanda ke da ƙwarewa a wannan ɓangare na gine-gine dama da sauran duk wani abu ɗaya kamata don kammala waɗannan gidaje ta yadda a nan gaba ba za a samu matsala ba. Don kuwa wannan haƙƙi ne da ya rataya a wuyan gwamnati na kawar da ire-iren waɗannan gidaje da ba a kammala ba, da ka iya zama barazana ga tsaro ko lafiyar al’ummar wannan ƙasa baki ɗaya. Idan muka yi la’akari da wasu daga cikin ƙasashen Afrika da dama, irin waɗannan gine-gine da aka yi watsi da su ba su da yawa, ’yan kaɗan ne idan muka kwatanta da na wannan ƙasa. Dalili kuwa, akwai haraji da ake sanya gidaje ko ana amfani da su ko ba a kammala gininsu ba, babu daga kafa wajibi ne sai kowa ya biya musu haraji kamar yadda doka ta tanada.

Yana da matuƙar muhimmanci a fara amfani da irin waɗannan dokoki a Nijeriya, dalili kuwa wannan zai bai wa duk wani wanda ke da irin waɗannan gidaje azamar kammalawa saboda ya san dole ne sai ya biya musu haraji. Sannan ita kanta gwamnati ya zama wajibi ta mayar da hankali wajen kammala waɗannan gine-gine nata da ta yi watsi da su, don ko babu komai za ta riqa samun kuɗin shiga ta hanyarsu. Babban abin mamaki da tsoro shi ne, me yasa irin waɗannan gidaje na Milyoyin kuɗi ake yin watsi da su? Lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya karɓi ƙasar nan, ya yi barazanar karɓe irin waɗannan gidaje ya miƙa su a hannun Jami’an tsaro don yin amfani da su a matsayin Hedikwatarsu ko kuma bai wa ma’aikata su shiga cikin su zauna kyauta. Ko shakka babu, yin hakan kan iya zama babbar maslaha ta magance matsalar, amma hakan bai yiwu ba saboda mafiya yawan masu waɗannan gidaje ’yan siyasa ne da ke kewaye da gwamnatin ta kowane ɓangare.

A ƙarshe, muna sake yin kira ga gwamnati, ta dubi buƙatar rage ko magance matsalar yawaitar waɗannan gine-gine da aka yi watsi da su a duk faɗin wannan ƙasa, waɗanda kai tsaye ke kawo mummunan barazana ga harkar tsaro da kuma asarar ɗimbin rayuka a lokacin da ya tashi rushewa, sannan Uwa-Uba ya zama wata matattarar ’yan ta’adda da ke watayawarsu a ciki.