Daga CMG HAUSA
Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya gana da shugaban majalisar gudanarwar ƙungiyar tarayyar Turai Charles Michel, da shugabar hukumar gudanarwar ƙungiyar, Ursula von der Leyen, a Beijing, da yammacin ranar 1 ga watan Afrilu.
Yayin ganawar, Xi Jinping, yayi cikakken bayani kan ra’ayoyi daban-daban game da yadda za a warware rikicin Ukraine a bisa yanayin da ake ciki a halin yanzu, na farko ya ce, ya zama dole a sa kaimi wajen lalibo hanyoyin zaman lafiya, da yadda za a daga matsayin tattaunawar sulhu.
Na biyu, a yi ƙoƙarin kandagarki na hana ƙaruwar girman matsalolin masu buƙatar tallafin jin kai. Na uku, a yi ƙoƙarin gina cikakken tsarin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a Turai da ma nahiyoyin Turai da Asiya. Na huɗu, ya ce dole ne a yi ƙoƙarin daƙile hanyoyin da suke haifar da ɓarkewar ƙarin tashe-tashen hankulla.
Fassarawa: Ahmad