Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamna Jihar Zamfara Bello Matawalle ya ce ƙwararan hujjoji sun nuna cewa manyan masu faɗa aji daga jihar na daga cikin waɗanda ke taimakawa ayyukan ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane a jihar.
“Wasu daga cikin waɗannan mutane jiga-jigai ne da jama’a ke mutuntawa, akwai kuma daga cikin jama’ar da ke karɓar ‘yan kuɗaɗe kaɗan domin bai wa ‘yan bindiga bayanai,” inji Gwamna Matawalle.
Cikin wata sanarwa da mai baiwa Gwamna Matawalle shawara kan harkakokin yaɗa labarai Malam Zailani Bappa ya fitar, ya ce hakan ne ya sa Gwamna Bello Matawalle ya kan yi rantsuwa da Alƙur’ani mai tsarki, ya kuma buƙaci waɗanda ke cikin gwamnatina da su yi hakan, domin nisantar da kansu daga ayyukan ‘yan bindiga a jihar.
Gwamna ya kuma yi kira ga duk ‘yan jihar da shugabannin siyasa da su bi sahun su domin tsaftace kansu daga duk wani zargi na mu’amala da ‘yan ta’adda.
Gwamnan ya qara da cewa, “duk waɗanda ke cikin gwamnatinsa sun ji kiran tare da rantsuwa da Ƙur’ani mai tsarki, face tsohon mataimakinsa da ya bijire wa matakin da ke zama hanya ɗaya tilo ta nisanta kai daga aikata laifin.
Matawalle ya ce ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin sun daƙile ayyukan ‘yan bindiga a jihar duk da goyan bayan da suke samu daga wasu ɓatagari, hasalima sun yi ƙoƙarin rage kaifin hare-haren ‘yan ta’dda a jihar.
“Ba sa son ’ya’yanmu su je makaranta, ba sa son mu yi tafiye-tafiye mu samu abin dogaro da kai, ba sa son mu samu zaman lafiya a gidajenmu da garuruwa da ƙauyukanmu, suna son mutane su yi tawaye ga gwamnatin jiha da ta tarayya. Amma ba za su yi nasara ba. Nasarar ta mu ce da yardar Allah Madaukakin Sarki.”
Gwamnan ya kuma ƙara jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu ta wannan mummunar ɗabi’a tare da roƙon iyalan waɗanda ‘yan ta’addan suka sace ‘yan uwansu da su amince da matakan da suke ɗauka don tabbatar da ceto ‘yan uwansu.
