PDP ta yi watsi da sakamakon zaɓen ƙananan hukumomin Jihar Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Katsina ta yi watsi da zaɓukan shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli da hukumar zaɓe mai zaman kanta a jihar ta shirya a ranar Litinin 11 ga watan Afrilu, 2022.

PDP ta bayyana zaɓen da karan tsaye ga mulkin dimokraɗiyya, abin takaici kuma abin kunya ga Jam’iyyar APC mai mulkin jihar.

Shugaban riƙo na jam’iyyar Hon. Salisu Lawal Uli ne ya bayyana haka a hedikwatar jam’iyyar dake birnin Katsina.

Idan za a iya tunawa Manhaja ta kawo labarin yadda hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Katsina, wato KATSIEC ta bayyana cewa jam’iyyar APC ce ta lashe zaɓen dukkan ƙananan hukumomin jihar guda 33 a cikin 34, inda ta soke sakamakon Ƙaramar Hukumar Dutsinma bisa dalilin da ta bayar na aikata ba daidai ba. 

Lawal Uli ya ci gaba da cewa, “muna kallon zaɓen a matsayin naɗin kantomomi ko kantomomi ne ai ba hukumar zaɓe ba ce za ta naɗa su, gwamnatin jiha ce ko ita ma gwamnatin jiha abu ne da ya saɓa wa doka, saboda akwai hukuncin kotun ƙoli da ya ce gwamnatocin jihohi ba su da hurumin naɗin kantomomi.”

Ya Kuma ce ba a yi zaɓe ba a ƙananan hukumomin Ƙanƙara, Ɓaure, Ɗan Musa, Jibiya, Rimi, Musawa, Ƙafur, Charanchi da kuma Bindawa.

A nashi martanin, tsohon gwamnan jihar Katsina a mulkin PDP Ibrahim Shehu Shema ya bayyana zaɓen da cewa abun kunya ne kuma abun takaici a ce jihar da shugaban ƙasa ya fito ta kasa shirya zaɓen ƙananan hukumomi ba tare da maguɗi ba.

Shema ya kuma yi zargi cewa an ƙi kai takardar rubuta sakamakon zaɓe a wasu ƙananan hukumomi, ya ƙara da cewa an rubuta wasu daga cikin sakamakon zaɓen a gidan gwamnatin jihar.

Ya kuma yi zargin cewa ba a gudanar da zaɓukan ba a wasu daga cikin ƙananan hukumomin, amma kuma an sanar da sakamako.

Daga nan, Shema ya sha alwashin cewar jam’iyyar su za ta ƙalubalanci zaɓen a gaban kotu saboda shugabannin Jam’iyyar APC sun kai ‘yan Nijeriya ƙasa.

Tsohon shugaban jam’iyyar kuma mai neman takarar gwamnan jihar Hon. Salisu Yusuf Majigi ya bayyana cewar idan irin zaɓen da aka yi a Katsina APC za ta shirya a shekara ta 2023 to ‘yan Nijeriya su shirya fuskantar ƙalubale, kuma ya ce sun tanadi dukkan wasu takardu da ke nuna cewar ba a yi zaɓen gaskiya ba a ƙananan hukumomin jihar, kuma za su yi amfani da su domin ɗaukar matakin shari’a.

Yakubu Lado, tsohon sanata kuma mai neman takarar gwamnan jihar, shi ma ya bayyana zaɓen a matsayin yaudara.

Sanata Lado ya ƙara da cewa da gangan APC ta shirya zaɓen don ta yaudari masu kaɗa ƙuri’a a jihar.

Lado wanda ya zanta da manema labarai a Ƙanƙara, ya yi zargin cewar APC da kuma jami’an tsaro sun hana al’ummar jihar zaɓen wanda suke so kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanadar.

Ya kuma zargi DPO na ƙaramar hukumar bisa yin awon gaba da wasu muhimman kayan zaɓe.

A nashi martanin sakataren gwamnatin jihar Katsina kuma mai neman tsayawa takarar gwamnan jihar a jam’iyyar APC, ya ƙaryata zarge-zargen da shugabannin Jam’iyyar PDP su ka yi, inda ya bayyana cewar ba a rubuta sakamakon zaɓe a gidan gwamnati ba kuma an kai kayan zaɓe a dukkan ƙananan hukumomin jihar tare da yin zaɓen a dukkan faɗin jihar.

Ya bayyana cewar PDP ce ta kai mutane a wuraren zaɓe don su hana zaɓen saboda sun san ba za su yi nasara.

Daga ƙarshe ya bayyana cewar PDP ta na zargin an yi ƙwange a zaɓen ne saboda haka suka riƙa yi a lokacin mulkin su.