Ruwan sama ya yi gyara a Cross River

Daga BASHIR ISAH

Aƙalla gidaje 463 ne suka lalace a tsakanin ƙananan hukumomi uku a jihar Cross River sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da aka samu a wasu yankunan jihar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), ya ruwaito cewa yankunan ƙananan hukumomin da iftila’in ya shafa su ne; Obudu da Yala da kuma Ogoja.

Jami’in Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) a shiyyar, Godwin Tepikor ya ce, an jagoranci tawagarsu a ranar Litinin inda suka ziyarci wuraren da lamarin ya shafa don gani da ido.

Jami’in NEMA ya shaida wa NAN cewa, “A yankin ƙaramar hukumar Obudu, mutane 503 ne lamarin ya shafa tare da lalata gine-gine 249 da sauran dukiyoyin jama’a.

“Haka nan a yankin ƙaramar hukumar Yala, mu ziyarci ƙauyuka biyar da ruwan ya yi wa ɓarna, wato Okpoma, Otuche, Olachor, Idigbo da kuma Igbekurikor.

“Mun kai ziyarar gani da ido ne biyo bayan rahoton neman ceto da Shugaban Ƙaramar Hukumar, Fabian Ogbeche ya aike mana.

Ya ƙara da cewa, “Iftila’in da ya auku a yankin a ranar 5 ga Afrilun 2022, ya shafi mutum 486 ne kana ya lalata gidaje 214 haɗe da dukiyo da bishiyo.”

Kazalika, Tepikor ya ce iftila’in da ya auku a yankin Ogoja ran 5 ga Afrilu, 2022, ya taɓa ƙauyuka da suka haɗa da Ishibori, Ukelle, Ogboje da kuma Abakpa.

A cewarsa, mutum 337 lamarin ya shafa a nan yankin, kana ruwa ya kwashe gidaje da dukiyoyi da dama.

Jami’in ya ce baki ɗaya, iftila’in ya shafi mutum 1,326 sannan ya lalata gidaje 463.