Shugaban Jam’iyyar ADC ya soki lamirin gwamnati

BABANGIDA S. GORA a Kano

An bayyana cewa da yawan shuwagabannin gwamnati a Jihar Kano ba su damu da matsalolin da suka shafi al’ummar jihar ba.

Hakan ya fito daga bakin muƙaddashin shugaban jam’iyyar ADC na shiyyar Arewa maso Yamma kuma sabon shugaban jam’iyar a Jihar Kano Hon. Musa Sha’aibu Ungoggo.

Ungoggo ya ce kasancewar Jihar Kano da take da yawan jama’a kimanin mutum sama da miliyan 20, akwai buƙatar a samu sauyin jam’iyyu guda biyu daga lokacin da aka fara dimukuraɗiyya ba a samu canji ba na jam’iyyun PDP da APC.

Shugaban ADC ya kuma ƙara da cewa yanzu akwai buƙatar kawo gyara da jama’a da yawa suke buqata a yanzu ya ba su damar ɗauko wannan jam’iya don manufofin da take da su suna kan tsari na taimakon al’umma ta fuskar ilimi, kasuwanci, tsaro da dai sauran su.

Sannan Musa ya ce lallai masu mulkin yanzu babu wani yunƙurin ganin sun taimaki jama’a da talakawa, don kuwa da suna da wannan batun ciyar da Jihar Kano gaba da tun farko an samu tagomashin gaske.

Haka kuma ya ce, “tunda aka fara shugabanci cikin Jihar Kano daga kan Malam Ibrahim Shekarau da ya fara tafiyar da mulkin dimukuraɗiyya, an yi titin State Road zuwa Ƙofar Nasarawa daga bisani Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi gadar sama.

“Haka zalika shi ma gwamna na yanzu ya matsa gaba kaɗan zuwa Dangi ya yi gadar sama da qasa tare da da kashe bilyoyin kuɗi amma har yanzu babu gwamnan da ya maida hankali kan batun ilimi a wannan jiha, inda kuma ya zama mun zama koma baya.”

Musa Ungoggo ya tabbatar da cewa daga cikin ayyukan da aka fidda biliyoyin nairori babu ɗan kwangila ɗaya da ya amfana da wannan aiki cikin ‘yan kwangilar jihar Kano, wanda sai da ya kai ga yashi ma idan banda ‘yan Chana din da suka yi kwangilar suna tsoron kada su je ɗauko shi da kansu a kora da sun kawoshi da kansu.

Shugaban ADCn ya kuma bayyana baƙin cikinsa na yadda gwamnatocin da suke mulki a baya da yanzu bisa yadda suka zura idanu kan matsalar ruwan sha take cin karenta babu babbaka  a jihar da yanzu haka a ƙasan gadojin da aka yi na milyoyin nairori za ka ga masu saida ruwa na baro sun mamaye ko’ina matsalar bata kau ba; maimakon gwamnati ta yi duba izuwa wannan fanni tare da magance wannan matsalolin ba gadar sama ba farko, inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *