Daga WAKILINMU
Mutum uku sun rasa rayuwarsu, wasu da dama sun jikkata a ƙaramar hukumar Offa ta Jihar Kwara sanadin wata budurwa.
Rahotanni sun nuna cewa, ƙungiyoyin ’yan daba biyu ne suka gwabza da juna biyo bayan wani saɓani da suka samu kan mace.
Rahoto ya nuna cewa, rikicin ya soma ne ranar Asabar. Wani mazaunin yankin, Alhaji Abdurrahman, ya shaida wa manema labarai cewa, rikicin ya kaure ne tsakanin ’yan daban tsagin Isale Oja da na tsagin Oja Oba a Offa.
A cewarsa, shugaban ɗaya daga cikin ƙungiyar ’yan daban ne ya kwace budurwan mamban ɗaya ƙungiyar ‘yan daban da suke hamayya da juna, hakan ya jawo rikicin.
Kakakin rundunar ’yan sanda reshen jihar Kwara, SP Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da mutuwar mutum biyu daga cikin ’yan daban, inda ya ƙara da cewa, a halin yanzun suna kan gudanar da bincike.
A wata sanarwa da ya fitar, kakakin ‘yan sandan ya ce, “kafin isar jami’an ‘yan sandan da aka tura zuwa wurin da abin ke faruwa, biyu daga cikin ‘yan daban da basa ga maciji da juna, Samad Adeyemi, ɗan shekara 21, da Abdulahi Mohammed, ɗan shekara 20, sun rasa rayuwarsu.”
“A halin yanzun dakarun ‘yan sanda na cigaba da gudanar da bincike kan lamarin,” inji shi.
