Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Jami’an hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) a yau Talata sun kai farmaki gidan tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha a Abuja.
Rahotanni sun bayyana cewa, ’yan jami’an da ake zargin sun zo ne ba tare da sammacin kame ba, sun dage cewa za su tafi da shi da ƙarfi, kamar yadda wani mai taimaka wa Sanatan Imo ta Yamma ya bayyana.
Okorocha wanda yana cikin ‘yan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar APC ya fuskanci matsaloli da dama da doka, ko dai daga hukumar EFCC ko kuma wanda ya gaje shi, Hope Uzodinma tun bayan da ya fice daga muƙamin gwamna.
Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, har yanzu bai yi magana kan lamarin ba har ya zuwa lokacin da ake cike wannan rahoto.
A ranar 29 da 30 ga watan Mayu ne aka shirya gudanar da zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar APC a dandalin Eagles Square da ke Abuja, babban birnin ƙasar.
