2023: Yadda al’ummar Bade/Jakusko suka raba gardama

Spread the love

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN

Masu hikimar magana sun ce: ‘Jummu’ar da za ta yi kyau tun daga Laraba ake tantanceta’. Haka kuma, ‘Ba a jayayyar bushiya da mai buzu (agalemi)’. Saboda a tarihin siyasar jihar Yobe ba a taɓa samun ɗan siyasar da jama’a suka haɗa kansu wajen tara kuɗaɗen aljihunsu domin sayen fam da hidima ga ɗan takara ba sai ta kan Hon. Sani Ahmed Kaitafi aka fara. Sannan shi ne matashin tilo wanda jama’a suka yi tsayin daka a kansa wajen cewa dolen-dole ko ta halin yaya sai sun tilasta shi ya fito takarar kujerar majalisar wakilai. Domin ya wakilce su a mazaɓar Bade/Jakusko a zaben 2023 mai zuwa. Saboda haka, ya kafa tarihin da shi kaɗai ya samu wannan tagomashi a tsakanin ‘yan siyasar jihar Yobe.

Haka ta la’akari da dandazon al’ummar da suka yi fitowar dango; ƙwansu da kwarkwata, inda jama’a suka nuna wa duniya cewa, lalle da gaske suke a matsayin nuna qauna da cikakken goyon bayan su ga ɗansu, kuma matashin ɗan siyasa wanda tauraruwarsa ke haskawa a sararin samaniyar jihar Yobe, Honarabul Sani Ahmed Kaitafi. Wanda a ƙarshen makon da ya gabata, (ranar Asabar) da ta gabata ne, a sa’ilin da ya zo gabatar da kansa ga shugabanin jam’iyyar APC a matakin mazaɓa da gundumomi, kana da ƙananan hukumomin Bade da Jakusko tare da bai wa al’ummar yankin tabbacin cewa ya shirya domin ci gaba da hidimta musu kamar yadda ya saba domin yin takarar kujerar majalisar wakilai, kamar yadda suka buƙata. 

Bugu da kari, wannan ziyara ce wadda ta shiga kundin tarihi, kuma ta buɗe sabon shafi na alƙiblar siyasar yankin kuma ta ƙara fito da al’amarin sarari da kore shakkun da ya tabbatar cewa lokaci ne ina matashi sabon jini, ɗan siyasa wanda ya ɗauki al’ummarsa a gadon bayansa tare da ganin ƙima da muhimmanci. Ya sake tabbatar da cewa zamani ne wanda al’umma su ka gaji da ragwayen wakilan da suka gaza sauke nauyin da aka ɗora musu. Saboda haka suka ga gara su jagoranci sauya alƙiblarsu da kansu ta hanyar zaɓa wa kansu mafita da kansu, musamman a ƙarƙashin manyan dattawan da al’umma ta shaida da dattaku wato, shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Lawan tare da Haziƙin Gwamnan jihar Yobe, limamin sulhu, Honarabul Mai Mala Buni, waɗanda kullum burinsu shi ne, samun matasa makamantansu Sani Ahmed Kaitafi a harkokin siyasa domin su kasance shugabanin gobe. 

Masu hikima sun ce, barewa ba ta gudu, ɗanta ya yi sassarfa. Honarabul Kaitafi yana daga cikin haziƙan matasan da al’ummar jihar Yobe ke alfahari da su, kuma masu basira ta musamman, waɗanda kowace al’umma ke bugun ƙirji da kasancewarsu mamaya gurbin shugabaninta. Kana kuma haka abin yake a zukatan waɗannan ƙwararrun shugabanin siyasar jihar Yobe da na ambata a farko, da ma ƙasa bakiɗaya.

Saboda sun koya, kuma sun haddace sanin makamar aikin gudanar da shugabancin al’umma daga kowanne mataki. Sannan sanin kowa ne cewa kulli yaumin babban burin Gwamna Buni shi ne, gina matasa domin kasancewarsu makomar kowace ƙasa. Gina matasa shi ne kyakkyawan ginin da ba zai yi tazgaro ba, sakaci kan haka, babbar matsala ce ga ci gaban kasa.

Kuma muna iya cewa wannan shi ne kyakkyawan burin da Sanata Lawan da Gwamna Buni suka dade suna dakon kasancewar sa, a matsayinsu na iyayen al’umma. Kuma masu kishin ci gaban al’umma ta hanyar gina matasan da za su gaje su bisa kyakkyawar turba. Wanda ana iya cewa, tun daga wannan rana ce, Sani Ahmed Kaitafi ya fassara mafarkin da waɗannan shugabanin ke fata ga al’ummar Bade da Jakusko, jihar Yobe da Nijeriya bakiɗaya.

Kuma abinda zai tabbatar maka da hakan shi ne, duba da yadda kowanensu ke tarairaya da jan matasa a jikin su. Da kuma irin yadda suka ga wannan ɗan zakin ya girma, musamman gamsuwar da zukatan jama’a suka bayyana na haƙiƙanin gaskiyar daidaiton kauna tsakaninsu da Honarabul Kaitafi, abin ya burge matuƙa, tare da Allah san-barka. Babu buƙatar dogon sharhi ga duk mutumin da ya halarci wannan taron ko idonsa suka gane masa ta kafafen yaɗa labarai, da na sada zumunta, zai kara yakini cewa Allah ne kaɗai ke haɗa wa mutum zukatan jama’a ba kuɗi ko wani abin Duniya ba. 

Bugu da ƙari kuma, masana sun tabbatar da cewa, Allah ne kaɗai ya isa ya haɗa zukata wuri guda ko ya tara wa mutum zukatan dubbai ko miliyoyin jama’a, kuma su ƙaunace shi, kamar yadda a ranar Allah ya haɗa dubun dubatar al’ummar zuwa ga ƙaunar Honarabul Sani Ahmed Kaitafi. Sannan duk wanda ya kalli wannan taron, ya san akwai kyakkyawan fata da annashuwan da ta bayyana mai cike da amincin dake tsakanin matashin ɗan siyasa da jama’ar Bade/Jakusko.

Kuma wannan ya tabbatar da cewa, bashi da madadi bisa dogon lokacin da ya ɗauka wajen sadaukar da duk abin da ya mallaka na lokaci, tunani da dukiya wajen ganin al’ummar wadannan kananan hukumomi a Bade da Jakusko daga aljihunsa. Saboda a wannan lokaci ba ya riƙe da wata kujera ko ofis da aka zaɓe shi, amma bai gushe ba yana ci gaba da hidimta wa al’ummar. Wanda hakan ya sa jama’a yankin shi suka yi masa abin da ba a tava yi wa wani makamancinaa ba a tarihin siyasar Yobe. 

A hannu guda kuma, ko shakka babu duk wanda ya zauna da Hon. Kaitafi zai gaya maka cewa Allah ya azurta shi da zuciya mai kyau, tausayi, hangen nesa tare da dattaku, baya ga qarancin shekarusa. Masu hikima sun tabbatar da cewa, akan hangi siffofin shugabanci ga mutum, a lokuta da dama tun yana a shekarun yarinta. Sannan kuma waɗannan halaye da siffofin shugabancin sun haɗa da hakuri, tausayi, bajinta da jajircewa, hangen nesa tare da dattaku, kyauta da karamci. 

Mutanen da suka yi mu’amalar yau da kullum da Sani Ahmed Kaitafi sun shaide shi da mutuntaka, karimci da halin dattaku, baya ga kyauta da jinkai ga masu karamin karfi (ana yi masa kirari da mai hannu duka dama). Har wala yau, jama’ar yankin Bade da Jakusko da sauran wasu yankunan jihar Yobe kowane lokaci suna tuna ayyukan alherin da ya aiwatar ga jama’arsa, waɗanda
suka shafi kowane ɓangaren rayuwa; harkokin ilimi, kiwon lafiya, ayyukan yi da yaƙi da zaman kashe wando. Ya taimaki manoma da tallafin kayan noma, gina masallatan Jummu’a, gina rijiyoyin burtsatse a yankunan karkara da birane domin inganta rayuwar jama’a.

Duk wanda ya nazarci rayuwar manyan yan siyasarmu a jihar Yobe, ƙarfin faɗa aji da suke da shi dangane da gudanar da mulkin jihar Yobe da ma a qasar Nijeriya bakiɗaya, Gwamnan jihar Yobe, Honarabul Mai Mala Buni, Shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Lawan da Alhaji Tijjani Musa Tumsa, ya san cewa shukar da suka yi ta yi ƙarfin gaske. Kuma zai ji a ransa cewa, hankulansu za su kwanta cike da alfaharin cewa sun samar da waɗanda za su ci gaba da gudanar da kyawawan ayyukan da suka shimfiɗa wa jama’a. 

A ɓangaren Honarabul Sani Ahmed Kaitafi, tsawon lokacin da ya ɗauka tare da waɗannan masu gidan nasa, tare da sauran abokan hulɗar yau da kullum; duk da Ɗan Adam tara yake, ba a taɓa jin kansu da masu gidansa ba. Kuma babu wata matsala da ta tava shiga tsakaninsu face alheri da biyayya cikin girmamawa tsakanin shi da su. Bari wannan batu, hatta abokanai da sauran jama’ar unguwa da gari, na ƙasa da shi, babu abin da yake tsakaninsabda kowa sai fatan alheri tare da Allah son barka ga rayuwarsa. Bugu da ƙari, kullum zancensa shi ne; ta wacce hanya zai bi don ya taimaki wani ko ya dasa wani mutum domin ya amfani kansa kuma al’umma ta mora.

Baya ga wacan babbar inuwar mahaifi (EInjiniya Ahmed Kaitafi), wanda kusan kowa ya san nagarta da dattakunsa a mahaifarsa, haɗi da ta waɗannan manyan jiga-jigai a jihar Yobe da Nijeriya. Halayen mutuntaka da suka bayyana na Sani Ahmed Kaitafi, suna ɗaya daga cikin ginshiƙin da ya ja hankalin al’ummar mazaɓar Bade da Jakusko wajen kiransa ya tsaya takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya. Saboda sun fahimci cewa, abubuwa guda uku suna da muhimmanci a ce mutum ya tara su a rayuwa. Waɗannan abubuwa su ne cikamakin samun babban rabo ga Dan Adam; Mutum ya samu iyaye na ƙwarai, iyayen gida maɗaukaka, tare da halaye nagari, wanda Allah ya tara masa. Waɗanda kowanne ɗaya babban arziki ne a sha’anin tafiyar da mulki ko wakiltar al’umma, kuma rashin su tazgaro ne ga rayuwa. 

Har’ila’yau, duk da yake shi Honarabul Sani Ahmed Kaitafi bai nemi wannan takara ba, amma jama’a suka yi tsayin daka ta hanyar dattawan siyasar yankin kan ya zo ya wakilce su. Kuma hakan yana daga cikin dalilin da ya sa al’ummar wannan yankin suka buƙaci Honarabul Kaitafi ya fito takarar majalisar wakilai tare da saya masa fam domin huce takaicin da suke da shi na rashin ingantaccen wakilcin da suka daɗe suna fuskanta. Sannan kuma abu na farko suna da yaƙinin cewa Sanata Ahmed Lawan, Gwamna Buni da uwar jam’iyyar APC a jihar Yobe za su duba halin da yankin ya daɗe a ciki tare da mutunta zaɓin al’umma, musamman a matsayin hakan shi ne ginshiqin mulkin dimukuraɗiyya da samun mulki nagari. Kana kuma kasancewar ƙaramar hukumar Bade ta ɗauki kimanin sama da shekaru 12 ba ta riƙe kujerar ba, tana hannun Jakusko. Duk da zance na gaskiya shi ne, wannan mazaɓar majalisar wakilai ta tarayya da ke wannan yankin ta na buƙatar canji nagari, musamman idan an kwatamta shi da takwarorinsa a wasu jihohi. 

Ƙananan hukumomin Bade da Jakusko suna daga cikin yankin da matsalar tsaron Boko Haram ta shafa a fakaice, musamman ta tuɗaɗar ‘yan gudun hijira da sauran abubuwan da matsalar ta haifar. Sannan yanki ne wanda Allah ya albarkanta da zama kan gavar kogin Yobe, hakan dama ce ga mazauna yankin wajen bunqasa ayyukan noma, kiwo, kamun kifi da sauran albarkatun da ake da su. Amma sakamakon rashin ingantaccen wakilci a matakin tarayya ya jawo an samu koma baya, saboda gazawar wakilin nagari.

Wallahi al’amarin ya daɗa zaburar da ƙaimin jama’ar Bade da Jakusko wajen samun hazikin wakilin da ya san hanya. Sakamakon da ya nuna Honarabul Kaitafi ne zai iya aikin, domin tun kafin a zaɓe shi ya saba; balle kuma ya samu cikakkiyar dama.
Kowace shekara Gwamnatin Tarayya ta na ware biliyoyin naira domin ayyukan raya mazaɓun da yan majalisar dattawa da na wakilai a kowane lungu da sakon ƙasar nan. Sai dai kash, ga dukkan alamu na Bade da Jakusko sun kasa kai bantensu. Wanda ba domin ayyukan raya mazaɓu da Sanata Ahmed Lawan yake aiwatarwa ba, da yankin ya samu gagarumin giɓi ta wannan fannin.

Saboda haka ne ya sanya masu raji da kishin Bade/Jakusko, suka fi mayar da hankali wajen zaƙulo haziqin mutum mai kishi da bai wa al’umma muhimmanci, kare mutunci da martabar da suka gada kaka da kakanni. Kuma a tsarin dimukuraɗiyya, Sani Ahmed Kaitafi ya cancanci shugabanci saboda jama’a shi suka nuna suna buƙatar ya wakilce su. Sannan duk wanda ya san ciwon kansa, ba zai taɓa wasa da diyaucinsa ba domin ƙwai a baka, ya fi kaza a akurki. Kuma a ci ba a sayarwa ba; zakara ya fi doki amfani. Sai dai kuma, abinda ya kamata Bade/Jakusko su duba shi ne, ba a cizon mumini sau biyu a rami ɗaya. Bugu da ƙari, mai rabon shan duka, baya jin kwava.

By Editor