Adadin motoci masu amfani da sabon makamashi ya zarta miliyan 10 a Sin

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Rahoton ma’aikatar tabbatar da kwanciyar hankalin jama’a ta ƙasar Sin ya nuna cewa, ya zuwa ƙarshen watan Yunin bana, jimillar adadin motocin ƙasar ya kai miliyan 406, inda daga cikinsu, motocin dake amfani da sabon makamashi mai inganci suka kai fiye da miliyan 10.01.

Kaza lika adadin sabbin motocin dake amfani da sabon makamashi da aka yi rajista a cikin watanni shida, na farkon shekarar bana a faɗin ƙasar, ya kai miliyan 2 da dubu 209, adadin da ya ƙaru da miliyan 1 da dubu 106, bisa na makamancin lokacin bara, wato ya ƙaru da kaso 100.26 bisa ɗari, wanda kuma ya kai matsayin koli a tarihi.

An lura cewa, adadin motocin dake amfani da sabon makamashi mai inganci da aka yi rajista a bana, ya kai kaso 19.90 bisa ɗari, cikin ɗaukacin motocin da aka yi rajistar su a shekarar.

Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa

By Editor