Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wani ango da amarya sun yi mutuwar kasko, bayan angon ya bulbula wa amaryar tasa fetur ya kunna mata wuta, ita kuwa ta ƙanƙame shi don su mutu tare.
Kamar yadda jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi, ya shaida wa manema labarai, lamarin ya faru ne ranar Asabar a Otun-Akute.
Tun farko dai amarya Lateefat ta bar gidan angon nata ne da ya aure ta shekaru uku da suka wuce, ta koma gidan maƙwabtansu saboda ta zarge shi da dukanta da kuma yi mata zagin cin mutunci.
Jaridar Punch ta ruwaito Oyeyemi, yana bayyana cewa, Adebanjo ne ya bi matar tasa zuwa wani gida da ta koma a unguwarsu. Ya tarar da ita tana sallah, ya kwara mata fetur ya cinna mata wuta.
Bayan ya cinna mata wuta, ita kuma sai ta yi kukan kura ta riƙe shi don su ƙone tare. Maƙwabtan ne suka ɓamɓare shi da kyar a hannunta.
Lateefat ta rasu bayan an kai ta asibiti ranar Asabar, yayin da shi ma Adebanjo, ya mutu ranar Lahadi awa 24 bayan ta rasu.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wutar da Adebanjo ya cinna wa Lateefat, har ta ƙona ƙafar ƙaramin ɗansu mai shekara biyu da haihuwa.
