Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Ƙungiyar Masu Gidajen Burodi ta Nijeriya (PBAN) ta ce, ta kammala dukkan shirye-shiryen fara yajin aikin kwana huɗu daga ranar Alhamis, 21 ga watan Yulin 2022, a duk faɗin ƙasar.
Masu sana’ar dai za su tsunduma yajin aikin ne don nuna damuwarsu kan yadda tsadar fulawa da sauran kayan haɗi ke ƙara tagayyara sana’arsu.
Shugaban Ƙungiyar na ƙasa, Emmanuel Onuorah da kuma mai magana da yawunta, Babalola Thomas, sun kuma roƙi Gwamnatin Tarayya da ta dakatar da cajinsu kaso 15 cikin 100 na fulawar da ake shigowa da ita Nijeriya.
Sun kuma nemi Hukumar da ke Tabbatar da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) ta rage tarar N154,000 da ta ke cin masu gidajen burodin da suka qi sabunta lasisin su a kan lokaci.
Ƙungiyar ta kuma roƙi gwamnati ta fara barin mambobinta su ci gajiyar rancen da Babban Bankin Nijeriya ya ke ba ƙanana da matsakaitan sana’o’i.
“Yanayin da muke sana’a a Nijeriya na tsadar kayayyaki ya kusa ya gurgunta masu sana’ar baki ɗaya. Galibinmu asara kawai muke tafkawa, hakan kuma ba abu ne mai ɗorewa ba.
“Burodi ɗaya ne daga cikin nau’ukan abinci mafiya aha da talaka da mai kuɗi ke amfani da shi. Saboda haka, ya zama wajibi gwamnatin Tarayya ta yi la’akari da wannan muddin tana so mu ci gaba da yin sana’a.
“A ƙoƙarinmu na tabbatar da ci gaba da ayyukanmu, mun yanke shawarar fara yajin aiki daga ranar Alhamis, 21 ga watan Yulin 2022, na tsawon kwana huɗu, in kuma muka ga ba a yi komai ba, za mu tsawaita shi zuwa abin da hali ya yi.
“Mun yi amannar cewa yin hakan ne zai sa gwamnati ta faka ta fahimci halin da muke ciki da kuma yadda muka jima muna haƙuri,” inji su.
