Mansur Gulma da magoyabayansa sun fice daga APC zuwa PDP

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Alhaji Mansur Adamu Gulma tsohon ɗan takarar ɗan majalisar dokoki a Jam’iyyar APC daga  ƙaramar hukumar mulki ta Argungu ya bar Jam’iyyar APC zuwa PDP tare da magoyabayan sa.

Sanata Dokta Yahaya Abubakar Abdullahi Mallamawan Kabi, Sanata mai wakiltar gundumar Kebbi ta Arewa shi ne ya karɓe su jiya Alhamis a garin Gulma ƙarƙashin jagorancin Alhaji Mansur Adamu Yargayra.

Alhaji Mansur Adamu Yargayra ya bayyana cewa dalilan da suka sanya su barin Jam’iyyar APC zuwa PDP sun haɗa da rashin adalcin da ake yi da kuma kama karya a Jam’iyyar APC a jihar Kebbi bakiɗaya. Saboda suna ganin suna riqe da madafun iko sukan karya ko ba gaba.

Bayan haka kuma ganin kakar zaɓen shekarar 2023 yana ƙaratowa babu wani abin a zo a gani da gwamnatin APC ta aiwatar a Kebbi wanda za a iya tinƙaho da shi wajen yaƙin neman zaɓe idan lokacin ya zo.

Ya ƙara da cewa yanzu haka sama da ƙungiyoyin matasan ‘yan kasuwa ashirin a wannan yankin sun dawo daga rakiyar tafiyar APC sanadiyyar barin Jam’iyyar APC da Sanata Dokta Yahaya Abubakar Abdullahi Mallamawan Kabi ya yi, inda dukkansu sun yi mubayi’a ga PDP.

Ya kuma yi kira ga shugabannin Jam’iyyar PDP da su cigaba da adalci tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar ba ta tare da nuna wani fifiko ba wanda ba shakka yin haka zai kai ta ga samun nasara a duk zaɓuɓɓuka ma su zuwa, kuma a shirye suke da su bayar da kowane irin goyon baya don ganin an kai gaci.

Da ya ke karɓar mutanen, Sanata Dokta Yahaya Abubakar Abdullahi Mallamawan Kabi ya bayyana jin daɗinsa bisa ga irin karimcin da ya ke samu a kullum safiya ta Allah daga al’ummar Jihar Kebbi bakiɗaya.

Ya bayyana cewa ayyukan da ya ke yi ba da kuɗinsa yake yin su ba kuɗin al’umma ne saboda haka riƙon amana ya zama wajibi ga duk mutumin kirki da mutane suka ga cancantarsa suka aminta da ya wakilce su.

Ya kuma yi kira  ga matasa da su kasance masu kishin kai musamman wajen bayar da gudunmawa ta ɓangaren siyasa saboda su ne ƙashin bayan kowace al’umma, saboda haka ka da su yi ƙasa a gwiwa wajen tabbatar da mallakar katin zaɓe.

Wata mai kama da wannan haka-zalika ranar Larabar da ta gabata ɗan majalisar dokoki mai wakiltar ƙaramar hukumar mulki ta Arewa Honarabul Sama’ila Salihu Bui ya karɓi shugabar mata  tare da waɗansu ‘ya’yan jam’iyyar APC daga ƙaramar hukumar mulki ta Arewa da suka canza sheƙa zuwa PDP. 

Kazalika daga ƙaramar hukumar mulki ta Shanga, Alhaji Shehu Na tsoffi tsohon Shugaban Ƙaramar Hukamar Mulki ta Shanga kuma tsohon mai bai wa Gwamna shawara da Honarabul Garba Hassan Warra tsohon shugaban ƙaramar hukumar mulki ta Ngaski kuma tsohon mai bai wa gwamna shawara, tare da Muhammad Bello Ganwo Shanga tsohon Sakataren ƙaramar hukumar mulki ta Kalgo da kuma Alhaji Isyaku Shanga sun canza sheƙa daga Jam’iyyar APC zuwa Jam’iyyar PDP tare da dubban magoyabayansu.