Yadda jam’iyyar APC ke tangal-tangal a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Tun bayan  tirka-tirkar zaɓen fid da gwanin yantakarar kujerar gwamna a jihar Kebbi Jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kebbi ta ɗauki hanyar rugujewa sanadiyyar rashin gaskiyar da mafi yawan ‘ya’yan jam’iyyar ke ganin an tafka da kuma irin yadda salon mulkin da ake yi da ya saɓa wa hankali.

Jihar Kebbi dai tana daga cikin jihohin da suka taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ganin jam’iyyar APC ta kafa gwamnati  a dukkan matakai. Tun kama daga ƙananan hukumomi zuwa jiha, har tarayya a shekarar 2015, lokacin da iskar guguwar Buhari ta kaɗa. Duk da yake dai tun a wancan lokacin zaɓen jam’iyyar APC bai yi wa waɗansu ‘ya’yan jam’iyyar daɗi ba amma dai saboda soyayyarsu da shi Buhari ɗin, suka haƙura suka bi bisa ga hasashen samun canji nagari.

Sai dai bayan da tafiyar ta soma tun ba je ko’ina ba, sai suka soma fahimtar an yi kitso da kwarkwata.

Bayan guguwar Buhari a shekarar 2015, jam’iyyar APC ta ƙara samun gagarumar nasara a jihar Kebbi sanadiyyar rashin tsayar da ɗan takarar da al’umma ke so a jam’iyyar PDP mai mulki a wancan lokacin.

Saboda haka, bayan kammala zaɓen fitar da gwani, sai gabaɗaya al’umma suka ƙara juya wa PDP baya, inda suka yi ta tururuwa zuwa APC, inda bayan an dawo APC kuma Sanata Atiku Bagudu da sauransu suka lashe zaɓen fidda gwani. Bayan da tafiya ta soma, sai ya rinƙa janyo ragowar  ‘yan adawa da suka saura a PDP, ya rinƙa ba su muqamai yayin da ainihin ‘ya’yan jam’iyyar APC suka koma ‘yan kallo.

A haka dai aka kammala zangon farko na mulki APC a ƙarƙashin jagorancin Sanata Atiku Bagudu duk da yake dai al’umma sun juya masa baya. A halin yanzu alqalumma suna ta nuna waɗansu alamu tun kama daga rashin halartar taruka ko waɗansu lamurra da suka shafi Atiku bisa ga la’akari da irin mulki na ‘yan uwa da abokai da yake yi da kuma mayar da waɗansu daga cikin shugabannin jam’iyya shanuwar ware bisa ga zargin biyayyarsu ga tsohon gwamnan jihar kuma Sanata mai wakiltar gundumar Kebbi ta tsakiya.

Wanda har wa yau shi ne jagoran siyasar Kebbi wanda daga baya aka rinƙa yi musu bita da ƙullin da ya yi sanadiyyar cire su daga muƙaman su da suka hada Arc. Bala Sani Kangiwa  shugaban jam’iyyar APC da Sakataren kuɗi da kuma ma’aji, Alhaji Garba Musa T/Marina. Yayin da jami’in hulda da jama’a Dakta Sani Dododo ya ajiye muƙaminsa bisa rajin kansa saboda hasashen shi ma tana iya zuwa kansa.

Haka zalika, shi ma kakakin majalisar zartasawa na jihar Kebbi Honarabul Sama’ila Abdulmuminu Kamba tare da waɗansu shugabannin majalisar an shirya wani kicin-kicin aka tsige su, inda aka maye gurabunsu da waɗansu, tare da yi musu alƙawarin sake takarar muƙamansu a karo na biyu saboda  biyayyar su ga gwamnatin Sanata Atiku Bagudu. 

Lamarin dai ya yi ƙamari har ya kai ga gurfana a gaban kotu dangane da cire su a kan muƙamansu, inda daga ƙarshe dai kotun ta yi watsi da qarar da waɗannan mutanen suka shigar.

Tafiyar siyasar Kebbi sai kullum kara tsani take yi musamman ƙaratowar zaɓen shekarar 2023 mai zuwa, inda Sanata Dakta Yahaya Abubakar wanda ke ɓangaren Sanata Adamu Aliero ya kunno kai don tsayawa takarar kujerar gwamna.

Yayin da shi kuma gwamna Atiku Bagudu ba ya da buƙata da haka, saboda sanin ba wani abin kirki da ya taɓuka a shekarun mulkinsa, duk da irin billiyoyin kuɗaɗen da ya karva daga gwamnatin tarayya saboda yana jin tsoron abinda zai iya biyowa baya na bincike.

Bayanai dai na nuna cewa, kusan shekara ɗaya ɓangaren Sanata Adamu Aliero ke ta faman neman maslaha, inda suka nemi waɗansu gwamnoni da dattawa zuwa shugabannin jam’iyya  don ganin Sanata Dakta Yahaya Abubakar Abdullahi ya samu zama ɗan takarar gwamna wanda kuma shi ne ɗan takarar mafi cancanta tare da cika dukkan sharuɗɗan da hukumar zaɓe da jam’iyyar APC suka gindaya.

Amma dai gwamna Atiku ya ƙi, kuma daga ƙarshe kuma aka zo zaɓen fidda gwani wanda shi ne ya zame wa jam’iyyar al’amari na ƙarshen neman duk wani sulhu ko shiri tsakanin ɓangarorin biyu. Kuma tun daga wannan lokacin a kullum safiya ta Allah jam’iyyar APC sai ƙara naƙasu take samu saboda barin jam’iyyar da ake yi babu ƙaƙautawa.

Tun bayan kammala zaɓen fidda gwani na kujerar gwamnan jihar da aka yi wanda har ma su ‘ya:yan jam’iyyar ta APC waɗanda ke da hankali sun nuna rashin gamsuwarsu bisa ga yadda aka gudanar da zaɓen, saboda bayanai sun nuna rashin sanin ya kamata.

Idan dai za a yi zaɓen fidda gwani a ce Sanata Dakta Yahaya Abubakar shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa a wancan lokacin bai sami quri’a ko ɗaya ba duk da irin ɗimbin magoya bayansa da kuma  ayyukan da ya aiwatar a ciki da wajen mazaɓarsa ta gundumar Kebbi ta Arewa. 

Haka zalika, tun a wannan lokacin magoya bayansa watau ɓangaren Sanata Adamu Aliero suka soma kiransa da ya bar jam’iyyar APC tare da Aliero din shi kansa. Inda bayan ‘yan kwanaki kaɗan Sanata Dakta Yahaya Abubakar Abdullahi  ta bakin mai ba shi shawara kan kafafen yaɗa labarai, Muhammed Jamil Yusuf Gulma ya sanar da barinsa jam’iyyar APC zuwa PDP kuma tare da kiran duk magoya bayansa da su ma su bar jam’iyyar kuma haka aka yi.

Tun bayan komawar waɗannan jiga-jigan siyasar Kebbi, a kullum safiya ta Allah daga ko’ina faɗin jihar sai tururuwa suke yi a cikin PDP,  inda har ma da waɗansu daga cikin waɗanda ke riƙe da mukaman siyasa tun kama daga matakan mazavu, zuwa ƙananan hukumomi, zuwa jiha da kuma kwamishinoni.

Yayin da waɗansu kuma suke ajiye muƙamansu, amma dai sai suka yi gum da bakinsu ba tare da cewa sun bar jam’iyyar ba. Amma dai mafi rinjayen hasashe yana nuna suna shirin haɗa nasu ya nasu.

A ɗaya ɓangaren kuma, su matasan da aka yaudara da sunan wannan gwamnatin za ta sama musu ayyukan yi da sana’o’i, sai gungu suke yi suna ƙona tsintsiya. A garin Yauri mahaifar Sakataren gwamnatin jihar Alhaji Umar Babale, wani gungun matasa sun ƙona tsintsiya tare da aikawa da gargaɗin kada APC ta kuskura ta zo wajensu neman kowace irin alfarma ta yanar gizo.

A farkon satin nan ma jam’iyyar APC ta sake tsunduma cikin ruɗani bayan da  tsohon mataimakin gwamnan jihar, Honarabul Bello Ɗantani Magajin Rafin Kabi ya rattaba hannu kan takardar ajiye muƙaminsa a matsayin shugaban hukumar ‘Direct Labour’.

Magajin Rafi ya bayyana cewa, ya ajiye muƙaminsa ne bisa ga ra’ayin kansa. Sai dai kuma abinda ya fi ɗaure musu kai shi ne, rashin gano alƙiblarsa. Shin ajiye muƙaminsa ne ya yi yana nan APC, ko kuwa a’a zai bar jam’iyyar ne?

Yanzu haka dai mafi yawancin ‘yan takarar muƙamai daban-daban ƙarƙashin tutar jam’iyyar APC a zaɓe mai zuwa na 2023. Cikinsu ya soma ɗurar ruwa sanadiyyar wandarewar da jama’a ke yi saboda suna ganin yadda iskar guguwar siyasa ta soma kaɗawa. Yayin da waxansu da ke riƙe da madafun iko suna cin zarafin waɗansu da suke ganin ba sa goyon bayansu.

A satin da ya gabata ma  shugaban ƙaramar hukumar mulki ta Argungu, Honarabul Salihu Ahmed KC ya yi sanadiyyar garqame waɗansu mutane biyar da suka haɗa da; Alhaji Haliru Karo Gulma da Sani Umar Na-Kafira da Sani Dogo da Basiru Kala da kuma Abdullahi Matumbuli saboda magoya bayan Sanata Dakta Yahaya Abubakar Abdullah ne wanda ya bar jam’iyyar APC zuwa PDP kwana nan.

Wannan koma-baya da jam’iyyar APC ke fuskanta a Kebbi dai masana sun ta’allaƙa shi da rashin iya mulki, da kuma rashin ganin girman kowa daga ɓangaren gwamna Atiku Bagudu.

A halin yanzu ya bar wa Alhaji Faruku Musa (Enabo) wanda shi ne babban hadiminsa dake kallon kansa a matsayin wani ɗan ƙaramin Allah dake iya kashewa da rayawa a fagen siyasar jihar ta Kebbi. Yayin da shi kuma gwamna Atiku ya ke ganin shi ne gwamna, shi ne ke ikon aiwatar da duk abinda yake so saboda haka yadda ya ke haka zai karya ko babu gaba.