Daga BABANGIDA S. GORA a Kano
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta yi nasarar yin awon gaba da masu laifuffuka daban-daban a faɗin jihar cikin watanni uku don samar da zaman lafiya da kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu.
Tabbatar da hakan na zuwa ne sa’ilin da rundunar take gabatar wa da manema labarai masu laifuffukan a hedikwatarta da ke Bampai a ranar Alhamis da ta gabata ƙarƙashin jagorancin Maigirma Kwamishinan ‘Yan Sanda da ake wa laƙabi da ‘Nagari Na Kowa’, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko.
A jawabinsa lokacin da yake gabatar da masu laifuffukan, kwamishinan ya yaba wa jami’an rundunar da sauran al’ummar dake taimaka wa wajen bada gudunmuwarsu a wannan hukumar kodayaushe.
A cikin waɗanda aka kamar sun haɗa da ‘yan fashi da makami mutum 42, tare da nasarar damƙe mutane 9 da ake zargi da garkuwa da mutane da karɓar kuɗin fansa, sannan rundunar ta kama aƙalla mutane 16 da laifin Damfara a Jihar Kano.
Sauran masu laifuffukan sun haɗa da mutane 27 da zargin laifin satar motoci da mashinan adaidaita, haka kuma akwai mutane 2 da rundunar ta kama da laifin safarar bil’adama, inda kuma ta samu nasarar cafke waɗanda ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi su 12.
Kazalika hukumar ta samu damar kama kimanin mutane 92 da ake zargi da aikata harkar daba da sara-suka a jihar tare da kuvutar da mutane 5 daga safarar su don aikin bautarwa zuwa wasu ƙasashen.
Haka nan rundunar ta samu nasarar karbe bindigogi daban-daban guda 25 da motoci guda 12 tare da kekunan adaidaita sahu guda 7 sai mashin mai ƙafa biyu guda 3, hakan nan ma rundunar ta karɓe wuƙaƙe guda 122 daga hannun masu laifi daban-daban.
Sauran abubuwan da aka samu sun haɗa da makaman da aka haɗa rodi kimanin guda 96 sai Parcels guda 269 da ɗaurin tabar wiwi guda 265 da ta kai darajar Naira miliyan biyu da dubu ɗari bakwai da ashirin da biyar.
Sannan akwai ƙananan kwamfuta guda 4 da wayoyin hannu guda 134 da kuma talabijin ƙirar Plasma guda 16.
Haka kuma rundunar ta samu nasarar gano ƙwayar Exol har kimanin guda 280 daga hannun waɗanda ake zargi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi, sai kwalaben madarar sukudaye guda 74 yayin gudanar da binciken.
Daga ƙarshe kwamishinan ya yaba da ƙoƙarin rundunar ‘yan sandan Jihar Kano da sauran ɓangarorin jami’an tsaro da ‘yan jarida da ma masu ruwa da tsaki bisa goyon bayan da suke ba hukumar wajen daƙile bara-gurbi a faɗin Jihar Kano da makwabtanta.