Muhimmancin mace a rayuwar al’umma

Daga SA’ADATU SAMINU KANKIA

Yana da matuƙar wuya wani mutum ya ce zai iya ƙayyade ko zayyana mahimmancin mata a cikin al’umma. Ba domin komai ba sai saboda alfanun da mata suke da shi a cikin rayuwar duniya ba za su lissafu ba.

Kama daga haihuwar mace har zuwa tsufanta, babu wani lokacin da bata bada gudunmawa ga al’umar ba.

Idan mu ka ɗauki ilimintarwa kawai, za mu ga cewa, gudunmawar da mata suke bayarwa a wannan fannin yana ɗauke kaso mafi rinjaye.

Tun bayan da yaro ya soma zama mace ke soma koya masa sauran abubuwan rayuwa na yadda zai zama mutum. Mata ne ke koyar da yara ciki da wajen makaranta. Hakan ya sa koyarwar da iyaye mata suke yiwa ‘ya’yansu a gida ya fi wanda ake musu a makaranta saurin shiga ƙwaƙwalwar yaro. Haka nan, kaso na mata masu koyarwa a makarantu na ko wani mataki mata sun fi yawa.

Gabaɗaya ita mace idan aka dubeta, Allah SWT Ya halicceta ne a matsayin mai karantarwa ko koyarwa.

Ba karantarwa ko koyarwa kaɗai ba, mata a kowacce al’umma suke kula da rainon yara, tsoffi da kuma jinyar mazajensu ko na kusa da su.

Juriya da ƙwarewar da mata suke da shi wajen yin rainon ƙananan yaran da ake bari a ƙarƙashin kulawar su zai yi matuƙar wahala ga namiji.

Dubi yadda mata suke kula da tsoffin da aka bari a ƙarƙashin kulawar su, musamman irin tsoffin nan da suke cikin matsala ta tsufa, cuta ko gudun hijira.
Yadda mace za ta yi jinyar mara lafiya ta kula da buƙatunsa tare da masa dara da wayo yadda zai ci abinci da amfani da magani maza ba su iya wa a cikin al’umma.

Wannan jinƙai da mata suke da shi ya sa a duk wata al’umma ake samun mata masu aikin jinya, ƙungiyoyin masu zaman kansu masu kula da yara ko gajiyayyu akasarinsu mata ne. Yaya al’umma za ta kasance idan aka ce babu matan da za su yi waɗannan ayyukan da maza ba su da jimirin iya yin su?

Mata suke bai wa kowacce al’umma kaso na kuɗaɗen shiganta. Duba da yadda mata suke da yawa a wajen ayyukan ofis da na kamfanonin kuma a albashi mafi ƙaranci da waɗannan ma’aikatun da kamfanoni suke samun kuɗaɗensu za a ga cewa mata sun fi yawa.

Haka nan mata suke riƙe da ƙananan sana’o’in da duk wata al’umma ta ke gadara da su. Domin ita mace bata raina jari, kuma bata da girman kai wajen duk wani sana’ar da zata yi domin ganin ta rufawa kanta asiri.

Babu shakka da wannan gudunmawar da mata suke bai wa kowacce al’umma, wannan al’ummar ta ke samun kuɗaɗen ta na shiga har ma ta ke samun gudanar da ayyukan ci gaba na wannan al’umar.

Babu shakka, jero ko lissafo mahimmanci ko gudunmawar mata ga al’umma ba zasu lissafu ba. Sai dai abin sani da fahimta shine, mata suke riƙe da al’umma. Duk al’ummar da ta bai wa mata dama da mahimmanci kuma da daraja, wannan al’ummar dole ta ci gaba ta samun ɗaukaka kuma ta samu tarbiyya a tsakanin mutanenta musamman masu taso wa da kuma raguwar munanan ayyuka a tsakanin matasa, irin su shaye-shaye, daba da karuwanci. Duk al’ummar da ta daraja mata, za ta ɗaukaka a idanun duniya.

Mace wani dausayi ce ta samun natsuwa da kwanciyar hankali ga duk wani xa namiji, duk iya tarin arzikinka, ko muƙami ko sarauta, ƙimarka ko mutunci ba ya cika sai kana da mata. Don haka mace ginshiƙi ce ta rayuwar al’umma.