Daga IBRAHIM YAYA
Sanin kowa ne cewa, duk ƙasar dake fatan samun ci gaba har ma a rika jin amonta a duniya, wajibi ne al’ummarta su zage damtse wajen ganin wannan buri ya tabbata.
Kamar sauran al’ummomin ƙasashen duniya, al’ummar Sinawa sun hada ƙarfi da ƙarfe wajen gina ƙasar Sin mai bin tsarin gurguzu mai sigar musamman ta ƙasar Sin a sabon zamani.
Gagarumin ci gaban da ƙasar Sin ta cimma a cikin shekaru 10 da suka gabata (2012-2022), sun haɗa da fannonin tattalin arziki, da binciken sararin samaniya, da fannin ƙirƙire-ƙirƙire da inganta muhalli da zaman rayuwar jama’a da sauransu.
Bayanai na cewa, ƙarfin tattalin arzikin ƙasar Sin ya kai wani sabon matsayi, ma’aunin GDPn ƙasar ya kai Yuan triliyan 114, adadin da ya kai kashi 18 bisa ɗari na ƙarfin tattalin arzikin duniya, wanda bai wuce kashi 11.4 bisa ɗari ba a shekarar 2012.
Masu iya magana na cewa, idan ka ga wane ba banza ba.
A waɗannan shekaru, ƙasar Sin ta ba da gudummawar kashi 30 bisa ɗari ta fuskar bunƙasuwar tattalin arzikin duniya, wadda ta kasance babbar ƙasar dake taimakawa ƙaruwar tattalin arzikin duniya.
Kana ta yi nasarar warware babbar matsalar fama da ƙangin talauci, wadda ta damu jama’ar Sin cikin dubban shekaru a baya.
Yanzu haka, akwai mazauna ƙauyuka kimanin miliyan 98.99 da suka yi ban kwana da ƙangin talauci.
Adadin ƙauyukan da suka sauya zuwa birane, ya ƙaru daga 53.1% zuwa 64.7%.
Mazauna ƙauyuka kimanin miliyan 180 sun ƙaura zuwa birane.
A matsayinta na ƙasar dake kan gaba wajen yawan masu amfani da intanet a faɗin duniya, kuma ɗaya daga cikin ɓangaren da ƙasar ta samu gagarumin nasara, ƙasar Sin na kan hanyar sauyawa daga yawan adadi zuwa raya harkar intanet mai inganci, da gina tsarin tafiyar da yanar gizo mai cike da tsaro, sakamakon kyautatuwar ababen more rayuwa masu inganci, da ci gaban fasaha da bunƙasar tattalin arziki na zamani. Haƙiƙa kasar Sin ta ciri Tuta.
Tsakanin waɗannan shekaru da muke batu, adadin masu amfani da yanar gizo a ƙasar Sin, ya ƙaru daga miliyan 564 zuwa fiye da biliyan 1.03, abin da ya sanya ta zama matsayi na ɗaya a duniya.
Ƙasar Sin ta samar da manyan hanyoyin sadarwa na 5G da layin fiber optic mafi girma a duniya. Kuma duniya ta shaida wannan nasara.
Darajar tattalin arzikin zamani na ƙasar Sin, ta tashi daga kudin Sin RMB yuan tiriliyan 11 kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 1.6 a shekarar 2012 zuwa yuan tiriliyan 45.5 a shekarar 2021, wanda ya sanya ta ci gaba da zama ƙasa ta biyu a duniya a cikin shekaru da dama a jere.
Yawan jimillar tattalin arzikin zamani a GDPn ƙasar, shi ma ya ƙaru daga kashi 21.6 cikin 100 a shekarar 2012 zuwa kashi 39.8 cikin 100 a shekarar 2021.
Hada-hadar cinikayyar Intanet ta ƙasar Sin da tsarin biyan kuɗi ta wayar salula, duk sun kasance a kan gaba a duniya.
Nasarorin da ƙasar Sin ta cimma a fannoni daban-daban, a wadannan shekarun da suka gabata, ba nasara ce kawai ga ƙasar Sin kaɗai ba, nasara ce ga duniya baki ɗaya.
Hakan ya ƙara jaddada cewa, sai an zubar da ruwa a ƙasa kafin a taka damshi.
