Magidanta idan Allah Ya hore ma ku, na gida ma su shaida – Farida Shehu Sa’ad

“Burina in ga fuskar maraya a cikin murmushi”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Tausayawa da nuna jin ƙai ga maraya abu ne mai matuƙar muhimmanci wanda addini ke ƙarfafawa, sai dai ba kasafai ake samun mutane masu nuna halin ya kamata wajen tallafa wa maraya ba, ko da kuwa na kusa da su ne ballantana wanda babu dangin Iya ba na Baba. Duk da halin ƙuncin rayuwa da akasarin ýan Nijeriya ke ciki, mutane irin su Hajiya Farida Shehu Sa’ad da ke zaune a Jos, na daga cikin ƙalilan ɗin mutanen da suka ɗauki al’amarin inganta rayuwar marayu da yaran talakawa da muhimmanci sosai. Ƙarƙashin ƙungiyar da take jagoran ta mai suna Alheri Danqo Ne, ta ɗauki nauyin karatun yara marayu da goya wasu mata da suka kai munzalin aure, duk kuwa da nauyin tarbiyyantar da nata yaran da ƙarancin shekarun ta. Wakilin Blueprint Manhaja a Jos, Abba Abubakar Yakubu, ya samu zantawa da wannan baiwar Allah da ta ce babban burinta ta ga murmushi a fuskar maraya.

MANHAJA: Ina son ki gabatar da kan ki ga masu karatu.
HAJIYA FARIDA: Sunana Hajiya Farida Shehu Sa’ad. Ni ‘ya ce ga Dr. shehu Sa’ad Guga da ke Tilden Fulani a Jihar Bauchi.

Yaya batun karatu da iyali?
Na yi karatuna na firamare da sakandire a Jos. Sannan na yi karatun Diploma kan yadda ake sarrafa na’urar Kwamfiyuta, kafin aka yi min aure. Sai daga baya ne kuma na je na yi karatun NCE don koyon yadda ake koyarwa a fannin Turanci da ilimin addinin Musulunci. Yanzu haka Ina da yara uku, Adam, Aliyu, Fatima.

Za ki iya tuna yadda ki ka taso da abin da ya fara sa miki tunanin ganin kin taimakawa mutane?
Mahaifina ya rasu tun Ina ƙarama, wato nima na taso a matsayin marainiya ne, sai dai ni ban san maraici ba, saboda na taso a cikin gata. ‘Yan’uwan mahaifiyata sun nuna kulawa da gata sosai. Ƙanin mahaifiyata Alhaji Ali shi ya riƙe ni kuma shi ya yi min duk wani abu da uba ya ke yi wa’ ýa’yansa. Da farko ma na zaci ko shi ya haifeni. Don ko a makaranta ma da Farida Aliyu nake amfani.

Har yanzu a cikin ƙawayena na makaranta akwai masu kirana da Farida Aliyu. Sai bayan da na da na je wajen ‘yan uwan mahaifina ne a Bauchi, za a saka ni a Babbar Sakandire a Kwalejin ‘Yan Mata da ke Bauchi wato G.G Bauchi shi ne suka ga duk takarduna da Farida Aliyu, a nan ne aka gaya min ai ga asalin sunan mahaifina. Tun daga sannan na cigaba da amfani da sunan mahaifina a jikin sunana, Farida Shehu Sa’ad.

Na taso Ina yabawa da irin kulawar da na samu, ta yadda har na girma ba a nuna min ni marainiya ba ce. Don haka idan na ga yara suna rayuwa cikin qunci da rashin samun kulawa don kawai su marayu ne, abin yana min ciwo sosai.

Kina daga cikin mata ƙalilan ɗin da ke da kishin taimakawa marayu, yaya ki ke samun ƙwarin gwiwar yin haka?
Gaskiya ne shi irin wannan aiki na jin ƙai kana yin sa ne don neman yardar Allah, amma kuma duk da haka kana buqatar ƙarfafa gwiwa, kuma Alhamdulillahi Ina samun ƙwarin gwiwa sosai daga iyalina musamman maigidana da kakata da kuma mahaifiyata. Sannan tallafin da nake samu daga wajen babana Dr Mustafa Inuwa, Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina da PS Abubakar ‘Yan Tumaki, shi ne yake ƙara min ƙarfi, saboda goyon baya da shawarwarin da nake samu daga wajen su. Ubangiji Allah Ya saka musu da mafificin alheri.

Yaya alaƙar ki take da sauran ƙungiyoyin cigaban rayuwar mata?
Babu shakka Ina da alaka da wasu ƙungiyoyin cigaban rayuwar mata daban daban saboda kishin da nake da shi na ganin an tallafa wa rayuwar raunanan mata da ƙananan yara. Yanzu haka akwai ƙungiyar da nake mai suna Mata Abin Alfahari Ne, inda yanzu haka muke kan haɗa kuɗi za mu gina rijiya da niyyar Allah Ya kai ladan kabarin waɗansu mambobin mu da suka rasu.

Akwai kuma yaransu da aka ɗauki nauyin karatunsu, kuma da yardar Allah shekara mai zuwa za su kammala karatunsu na sakandire, inda nan ma za mu biya musu kuɗin jarrabawar fita, in sha Allah. Har wa yau ina cikin ƙungiyar Ƙasaitattun Mata, wacce ita ma ƙungiya ce ta tallafawa cigaban mata da taimakon marayu. Nan ba da daɗewa ba in sha Allahu muna shirye shiryen kai ziyara a gidan marayu, domin ba su tallafi, daga ɗan abin da muka tattara na gudunmawa a tsakanin mu.

Ke ma na ji kina da wata ƙungiya ko gidauniya ce ta taimakawa marayu ko?
E, haka ne. Ina da wata Gidauniyar taimakawa marayu da marasa ƙarfi da muka kafa ni da wasu mutane ana ce mata Alheri Danƙo Ne Charity Foundation, kuma ni ce nake shugabantar ƙungiyar.

Alhamdulillah, muna ba da tallafin karatu da raino ga wasu yara marayu da ke gaban mu, wanda muke riƙe da su tare da yaran mu. Nima hannu na yanzu haka akwai marainiyar da na riƙe kuma zuwa ƙarshen wannan watan zan yi mata aure. In sha Allahu ni ce na dauki nauyin komai, sai kuma gudunmawa daga ýan uwa da masoya.

Yaya ki ke ganin halin rayuwar da wasu mata ke ciki, sakamakon gazawar mazajensu da yanayin tsadar rayuwa, wacce shawara za ki ba su?
Babu shakka yanzu rayuwa ta yi tsanani sosai, masu halin ma suna kuka da yadda abubuwa ke tafiya, ballantana masu ƙaramin ƙarfi da talakawa. Gaskiya a irin wannan yanayi dole a jinjinawa maza saboda ƙoƙarin da suke yi wajen ganin sun samar wa iyalinsu abin da za ci, a rufawa kai asiri.

Shi ya sa koda yaushe nake jan hankalin mata ýan’uwana mu kama sana’a, mu kuma ci gaba da haƙuri da zaman gidan mazajen su. Don shi zaman gidan miji dole sai da haƙuri, tun da ma haka iyayenmu suke gaya mana, ballantana yanzu da rayuwa ta zama abin da ta zama. Su ma kuma maza su riƙa tausayawa matansu, idan Allah Ya hore musu na gida ma su shaida, wannan shi ne zaman tare.

Wanne abu ne za ki so a riƙa tunawa da ke, dangane da taimakon da ki ke bai wa marayu da mabuƙata?
Gaskiya Ina afahari da abubuwan da alheri da kawo yanzu Ubangiji ya nufe ni da yin su, Ina kuma roƙon Allah Ya ja kwana na ya ƙarfafa zuciyata, in ci gaba da ayyukan alherin da na fara. Ina fatan za a tuna da gudunmawar da na bayar wajen ɗaukar nauyin biyan kuɗin karatu da rainon yara marayu da na yi.

Wanne taimako ƙungiyar ku ke buƙata don ta ci gaba da ayyukan da take gudanarwa?
Kungiyata na buƙatar abubuwa da dama na tallafi daga al’umma. Ka ga a yanzu ni ce nake ɗaukar dawainiyar akasarin abubuwan da muke yi, sakamakon yadda ake da ƙarancin masu tallafawa ayyukan ƙungiyoyi irin namu a Jos.

To, kuma da yake ina da mutane na a wasu garuruwa daban daban irin su Kano, Kaduna, Katsina, Kebbi, Yobe, da kuma Yola, a haka nake samo taimako da ɗan gudunmawar da za a tafiyar da wasu harkokin. Wani lokaci kuma mu kan sa wa kan mu tara ne, kowa ya ba da wani abu na taimako da za a yi aikin ƙungiya da shi.

Wacce nasiha za ki yi wa wasu iyaye musamman mata game tarbiyyar yara marayu da aka ba su alhakin riƙewa?
Wannan tambaya ta tuna min da wani al’amari da ya faru kwanaki a nan Jos, inda aka gano yadda wata mata take dukan ýaýan mijinta, tana azabtar da su. Mutanen anguwar suna mata magana a kan kuskuren abin da take yi, sai ta riƙa zagin su, tana faɗar maganganu marasa daɗi.

Da maganar ta zo kunnena, ba shiri haka na je har sai da muka zauna da Mai Anguwarsu, aka ɗauki matakin da ya dakatar da ita kan abubuwan da take yi, kuma muka sa wasu mata su riƙa sa ido suna lura da abubuwan da take yi wa yaran.

Babu shakka akwai abin takaici game da yadda wasu iyayen ke wofintar da al’amarin tarbiyyar yaransu, suna mantawa cewa, amana ce aka ba su, kuma ubangiji zai tambaye su kan abin da suka shafi rayuwar iyalinsu. Ba a wasa da al’amarin maraya ko kaɗan.

Idan za ki samu dama wanne abu ki ke so ki yi wanda zai kawo sauyi a rayuwar mata da ƙananan yara?
Babban burina a har kullum shi ne in ga rayuwar mata ta inganta, su samu ilimi da sana’o’in dogaro da kai. Su kuma yara marayu, ina son kullum in riqa ganin murmushi a fuskar su, su samu abinci da sutura, su samu ilimi da dukkan wata kulawa da suke buƙata a rayuwarsu. Idan Ina da dama to, komai na mallaka zai tafi ne wajen kyautata rayuwar mata da ƙananan yara.

Wanne abu ne ya fi ɗaukar hankalinki a lokacin da ki ke cikin nishaɗi?
In ga fuskar maraya cikin nishaɗi da walwala.

Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwarki?
Babu Maraya Sai Rago, da kuma Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara!

Mun gode.
Ni ma na gode kwarai.