Tafiyar Shekarau da Kwankwasiyya: Tarihi ne yake neman maimaita kansa

Daga MUKHTAR MUDI SIPIKIN

Jiya na ke jin wani labari, wai Shekarau zai bar NNPP ya koma wata jam’iyar, gaskiya ne ko ba gaskiya ba ne? Ni dai ba ni da tabbaci, amma in ya zama gaskiya ne, to ma iya cewa tarihi na neman maimaita kansa kenan.

Lokacin yaƙin basasar Kano tsakanin Tukurawa da Yusufawa; Yusufawa ba su samu sarautar Kano ba, sai suka fice daga Kano su kai sansani a wajejen Takai.

Daga nan suka haɗa runduna don su shigo Kano su ƙwaci sarautar Kano, don su ƙara ƙarfi sai suka dinga tura wasiƙu wajen Sarakuna irin su Gumel, Haɗejia da Ningi don su dafa musu, su ci nasara.  

A haka ne Sarkin Ningi ya amsa kira ya taho suka haɗe. Sai dai shi dama ba wani shiri yakwe da Kano ba. Don haka dama ta samu, gashi zai haɗa kai da ‘yan Kano a farmaki Kano (buri ya cika).

Su kuma Yusufawa sun san niyyarsa kuma su ma suna da nasu lissafin, don sun san ko da sun ci nasarar ƙwace Kano, to tabbas gaba sai sun yaƙi Sarkin Ningi don ba wani shiri za a yi ba.

Ana haka sai Sarkin Gumel ya amsa kiransu ya zo da runduna da kayan yaƙin da ya fi na Sarkin Ningi, dama ta samu ga Yusufawa. Kawai sai aka tsara yadda za su shigo Kano, sai aka ce Sarkin Ningi shi zai kasance a gaba da rundunarsa.

Sun yi haka ne, don da an fara yaƙi, a gama da shi da rundunarsa; kenan sun jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya. Idan suka ƙwace Kano, sannan aka kashe Sarkin Ningi to shikenan, buqata ta biya, gaba ba su da matsala ko barazana da Ningi.

Ashe shi ma Sarkin Ningi ya lura da maƙarƙashiyar da ake shirin yi masa. Tsakar dare kafin a je yaqi, ya sulale da shi da rundunarsa, ya bar Yusufawa su ƙarata. Bayan sun ci yaƙin kuma, ya yi ta kawo musu harin bayan fage.

To ƙila su ma ‘yan Kwankwasiyya na son su haɗa kai da abokin adawarsu Shekarau ne su yaƙi APC, idan sun ci nasara to shi kenan, sai a murƙushe Shekarau.

Tunda an ce wai gabaɗaya ‘yan majalissar tarayya da na jaha 40 ba yaronsa ko ɗaya, idan har ta tabbata haka, an ɗaura ɗambar rushe gidan siyasarsa. Wato  ‘yan Kwankwansiyya sun jefi   tsuntsu biyu da dutse ɗaya kenan kamar yadda Yusufawa su ka so yi kenan.

Idan kuma Shekarau ya koma wata jam’iyar, to ya maimata abinda Sarkin Ninigi ya yi shi ma kenan. Lokaci dai aka ce alƙali!

Mukhtar Mudi Sipikin, shine xan takarar Majalissar Tarayya ta Ƙaramar Hukumar Fagge da ke Jihar Kano a ƙarƙashin tutar Jam’iyar PRP Nasara! (Nasara ta Allah ce).