Xi ya ƙarfafa gwiwar ƙwararrun ƙasashen waje da su ƙara bada gudummawa wajen inganta mu’amala tsakanin Sin da sauran ƙasashe

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya ƙarfafawa ƙwararrun masana harsunan waje a fannin wallafe-wallafe gwiwa, da su ƙara ba da gudummawa wajen inganta yin musaya da sadarwa tsakanin Sin da sauran ƙasashen duniya, da gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga ɗaukacin bil-Adama
Xi ya bayyana hakan ne jiya Alhamis a cikin wata wasiƙa da ya aike wa wadannan ƙwararrun na ƙasashen waje, yayin da kamfanin wallafa littattafai ke cika shekaru 70 da kafuwa.

Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa

By Editor