Yusuf Buba Yakub ya yaba da matakan da Ƙasar Sin ta ɗauka na taimaka wa Afirka

Daga CMG HAUSA

Shugaban kwamitin kula da harkokin waje na majalisar wakilan Nijeriya, Yusuf Buba Yakub, ya bayar da sanarwa a kwanan baya, inda ya bayyana cewa, yadda ministan harkokin wajen ƙasar Sin Wang Yi, ya sanar da soke basussuka 23 da ƙasar ke bin wasu ƙasashen Afirka 17 ba tare da kuɗin ruwa ba, ya kasance wani ƙarin matakin yaba wa tun bayan shekarar 2000.

Mr.Wang Yi ya sanar da hakan ne, lokacin da yake halartar taron masu aikin tabbatar da sakamakon da aka cimma, a taron ministoci karo na takwas na dandalin tattaunawar haɗin gwiwar Sin da ƙasashen Afirka.

Ya kuma kara da cewa, zuwa shekarar 2019, gaba ɗaya, gwamnatin ƙasar Sin ta soke basussukan da take bin ƙasashen Afirka, da suka kai dalar Amurka biliyan 3.4, matakin da ya shaida dankon zumuncin da ke tsakanin Sin da al’ummar Afirka.

Yusuf ya ce, baya ga soke basussukan da take bin ƙasashen Afirka, ƙasar Sin tana kuma ta ƙara shigar da kayayyaki daga ƙasashen Afirka, inda ta amince da ƙasashen Afirka su fitar da kayayyakinsu zuwa Sin ba tare da sanya musu kudin kwastan ba, don tallafa wa ƙasashen Afirka ta fannonin bunƙasa ayyukan gona da na kere-kere, tare da kuma faɗaɗa haɗin gwiwarta da ƙasashen Afirka, ta fuskokin tattalin arzikin zamani, da kiwon lafiya, da kiyaye muhalli da sauransu.

Ya ce waɗannan matakai da gwamnatin ƙasar Sin ta ɗauka a jere matakan diplomasiyya ne na sada zumunta, waɗanda suka samar da misali ga sauran ƙasashen duniya.

Fassarawar Lubabatu