Wariyar launin fata ta fi cuta ɓarna

Daga MINA

Shugaban kwalejin kiwon lafiyar al’ummar Amurka ta jami’ar Rutgers Mr. Perry Halkitis, ya taɓa bayyana cewa, ana fuskantar wariyar launin fata game da rarraba alluran rigakafi a ƙasar.

Yau “duniya a zanen MINA” na zana wani Cartoon game da wannan matsala.

Cibiyar kandagarkin cututtuka ta Amurka, ta ba da ƙididdiga kwanan baya, wadda ke cewa, mutane masu fama da cutar ƙyandar biri a ƙasar, yawancinsu masu tsatson Latin Amurka, da na Afrika ne, wanda suka kai kashi 33% da 28%.

Amma, alal haƙiƙa, wannan adadi ya fi yawa a wasu jihohi ko birane.

Abin baƙin ciki shi ne, al’ummu masu tsatson Latin Amurka da na Afrika, ba su samu isassun alluran rigakafin cutar ba.

Perry Halkitis ya ba da tabbacin cewa, ana fuskantar wariyar launin fata kan rarraba allurar rigakafi.

Farar fata sun fi samun allura bisa na masu tsatson Latin Amurka da na Afrika.

A cikin waɗannan shekaru da suka gabata bayan ɓarkewar cutar COVID-19 a duniya, al’ummar kananan ƙabilu a Amurka sun sha fama da rashin adalci a fannin ba da jiyya, abin da ya jawo hankalin mutane sosai.

A halin yanzu kuma, annobar ƙyandar biri ko monkeypox, na sake yin kashedi kan Amurka da cewa, dole ne a duba matsalar wariyar launin fata.

Rayukan ko wane mutum na da daraja, duk da launin fatansu ya bambanta, kowa na da haƙƙi iri daya a duniya, ciki har da haƙƙin samun allurar rigakafin.

Mai zane: MINA