An kori sojojin da suka kashe Sheikh Goni Aisami a Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu

Rundunar Sojojin Nijeriya ta bayyana ɗaukar matakin korar wasu sojojinta biyu bisa samun su da laifin kashe malamin addinin Musulunci, Sheikh Goni Aisami Gashuwa, a jihar Yobe.

Sojojin da lamarin ya shafa su ne Lance Kofur John Gabriel da Lance Kofur Adamu Gideon.

Sanarwar korar ta fito ne daga muƙaddashin kwamandan da ke kula da Bataliya ta 241 dake Nguru a jihar Yobe, Laftanar Kanar Ibrahim Osabo, inda ya shaida wa manema labarai cewa kwamitin binciken haɗin gwiwa da aka kafa tare da haɗin gwiwar ‘yan sanda ya same su da laifi.

Ya ƙara da cewa, an sallami waɗannan sojojin biyu ne saboda tuhume-tuhume guda biyu da aka same su da su; na rashin yin aiki bisa ƙa’ida da kuma nuna ƙyama ga horon soji da suka samu.

Bugu da ƙari, Laftanar Kanar Osabo ya ce za a miƙa sojojin da aka kora ga hannun ‘yan sanda a jihar Yobe domin gurfanar da su a gaban kotu bisa laifukan da suka aikata.

A makon da ya gabata ne waɗannan sojojin suka yi wa Sheikh Goni Aisami Gashuwa kisan gilla kusa da garin Jaji-maji, shalkwatar ƙaramar hukumar Karasuwa, a kan hanyarsa daga Kano zuwa gida Gashuwa.

Al’ummar gari haɗi da ‘yan sanda a Jaji-maji ne suka samu nasarar kama sojojin wanda daga bisani aka gabatar da su a ranar 23 ga watan Agustan 2022, da ake zargi da hannu a kisan Malamin.

Mai magana da yawun Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Yobe, DSP Dungus Abdulkarim, a wata zantawa da wakilinmu ta wayar tarho, ya ce sun kama waɗanda ake zargin ɗauke da bindigogi ƙirar AK-47.

Haka kuma, Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da kisan inda ya buƙaci a gaggauta hukunta sojojin da suka aikata kisan.