Samar da isasshen taki kuma mai rahusa ga manoma

Manoman Nijeriya, kamar sauran takwarorinsu na sauran ƙasashen Afirka na kokawa da ƙarancin taki, ɗaya daga cikin muhimman kayayyakin amfanin gona da ake buƙata domin magance ƙalubalen da ke kunno kai ga yunwa a ƙasar musamman ma nahiyar Afirka baki ɗaya.

Sauyin yanayi da sauran abubuwa na yin mummunan tasiri a kan ƙasa wajen tilasta buƙatar takin zamani don taimakawa wajen bunƙasa amfanin ƙasa don ingantaccen amfanin gona. Ƙarin amfani da taki ya ba da gudummawa sosai wajen haɓaka samar da abinci da tabbatar da wadatar abinci.

A Nijeriya rashi ko ƙarancin takin zamani na daga cikin matsalolin da manoma ke fuskanta wajen gudanar da harkar noma a ƙasar.

Gwamnatoci a matakai da dama kama daga matakin tarayya zuwa na jihohi sun sha ikirarin samar da taki mai rahusa ga manoma.

Amma wasu manoman ƙasar, waɗanda galibinsu masu ƙaramin ƙarfi ne na kukan cewa ba su gani a ƙasa ba.

Sakamakon matsaloli irin na cin hanci da rashawa da kuma wasu bambance-bambance irin na siyasa da ake zargin sun mamaye harkar rabon taki a ƙasar. Kuma wadannan matsalolin, a cewar ƙwararru na janyo giɓi ga irin amfanin gonar da manoman ke samarwa.

To sai dai kuma, a ɓangaren noman zamani kamar yadda takin zamani ke zama abu ne da ba za a iya samu ba, kuma ya kasance abu ne wanda manoma masu matsakaita da masu ƙaramin ƙarfi a Nijeriya ba za su iya samu ba saboda tsadar kayan masarufi da kuma yadda ake siyasantar da rarraba shi. Kamar yadda aka yi a ƙidaya na ƙarshe, masana’antu sun tabbatar da cewa farashin kayayyakin ya yi tashin gwauron zabo da buhun NPK da Urea da ya haura Naira 20,000 a kasuwa.

Abin baƙin ciki shi ne, tallafin da gwamnatocin jihohi ke bayarwa ta hanyar tallafin farashin taki ko dai babu shi ko kuma ana ha’intar manoman wajen ba su irin wannan tallafin. Tabbas, wannan ya qara dagula rikicin kuma ya sanya samfurin yin ɗan karen tsada, kuma samunsa ga talakan manomi ya zama matsala.

Mun damu cewa ƙarancin taki ya sa ya zama haɗari biyu ga talakawan Nijeriya manoma da ke fama da ’yan bundiga da sauran miyagun laifuka. Wani abin damuwa na neman sa noma ya gagara. A yayin da ya ke fuskantar rashin samuwa da hauhawar farashin takin da kuma halin da ake ciki, manomi na fuskantar rashin tabbas na rashin amfanin gona a lokacin girbi.

A kwanakin baya ne babban sakataren ƙungiyar masu samar da takin zamani ta Nijeriya (FEPSAN), Gideon Nagedu ya yi ikirarin cewa, ƙarancin sinadarin Urea ne kawai, wanda ya ce giɓin da ake samu ya samo asali ne daga kamfanonin da ake nomawa. Amma bayanan da aka samu ciki har da damuwar da yawancin manoma suka nuna, ya bayyana a sasari cewa, ƙarancin bai iyakance ga Urea kawai ba har da sauran nau’ukan.

A baya dai an tava zamanin da takin zamani ba wani kayan gabas ba ne a wajen manoma a Nijeriya sakamakon yadda aka wadata ƙasa da shi, inda a wasu ɓangarorin ƙasar ma kusan rarrashin manoma ake yi tare da kai musu takin kusa da gida ana koya musu dabarun sarrafa shi.

An gina qananan ma`aikatun gona a yankunan karkara kana aka shake su da taki da iri da sauran kayan aikin gona da malamai.

Amma daga bisani sai taki ya zama zuma, sannu-a-hankali ya fi ƙarfin ƙananan manoman ƙasar, waɗanda su ne sama da kashi saba`in bisa ɗari na manoman Nijeriya.

Saboda karancin taki a Nijeriya, har ta kai ga wasu ’yan siyasa na alƙawarin samar da taki a lokutan yaƙin neman zaɓe.

Gwamnati, kama daga matakin tarayya da jihohi sun sha ikirarin wadata manoma da takin zamani, amma har yanzu dai kukan rashi ko ƙarancin takin zamani shi ne ƙorafin da ƙananan manoma ke yi a kusan mafi yawan jihohin Nijeriya.

A halin yanzu, wannan jarida tana ganin ya dace gwamnati ta tashi tsaye wajen shawo kan wannan matsalar. Misali, yaya tasiri da kyakyawan ayyukan da ake yi na hada-hadar taki a ƙasar? Waɗanne ƙalubale ne ke hana tsire-tsire yin aiki? Waɗannan su ne ainihin batutuwan yayin da al’ummar ƙasar ke ƙoƙarin warware matsalar ƙarancin kayan amfanin gona mai matuƙar muhimmanci.

Yana da kyau a ce zuba jarin noman taki ba wai kawai zai taimaka wa Nijeriya wajen dogaro da kanta wajen samar da abinci ba, har ma zai taimaka mata wajen bunƙasa tattalin arzikinta da kuma tabbatar da wadatar abinci. Wataƙila ya dace a yaba wa wannan shiri na Dangote bisa jajircewarsa na ƙarfafa samar da taki a cikin gida a Nijeriya ta hanyar gina takin zamani na dala biliyan 2.5.

Mun yi imanin, kamar yawancin ’yan Nijeriya, idan takin Dangote ya fara aiki sosai, zai taimaka sosai wajen ganin Nijeriya ta dogara da kanta wajen samar da taki tare da fitarwa zuwa wasu ƙasashen Afirka da sauran sassan duniya.

Babu shakka ana samun ƙaruwar buƙatar taki a Nijeriya. Mayar da wannan buƙatu ta hanyar samar da samfurin da kuma samun rahusa ga manoma zai gaggauta yunƙurin da al’ummar ƙasar ke yi na samar da abinci mai ɗorewa.

Idan an yi la’akari da ra’ayinmu, gwamnati ta yi magana game da sha’awar mayar da hankali kan noma a matsayin babban abin da ke haifar da ci gaban al’amuran al’umma zai iya yin ma’ana ne kawai idan an magance duk wata matsala ta samun taki da sauran kayan amfanin gona. Ciki har da kutse daga mutanen da aka fallasa a siyasance. Wannan al’amari ya ci gaba da zama cikas ga samar da taki, rarrabawa da amfani.

Akwai dalilai daban-daban da ya sa gwamnati ba za ta iya yin watsi da harkar noma ba. Wannan sashe a halin yanzu yana aiki a matsayin babban sashi. Da kusan kashi 33 cikin 100 na rashin aikin yi, Nijeriya ba ta da wani zaɓi illa ta baiwa noma fifiko saboda yuwuwarta na samar da ayyukan yi da kuma inganta harkar samar da abinci.

Ga dukkan alamu dai idan ba a sake lale tare da kau da son zuciya a harkar samar da takin zamani a Nijeriya ba, to ga alama takin zamani ka iya zama ƙaron kalgo ga manoma, kuma burin Nijeriya na wadata ƙasa da abinci ka iya ci gaba da fuskantar ƙalubale.