Abin damuwa ne matuƙa yadda aka gaza shawo kan yaƙin Rasha da Ukraine – Guterres

Babban Magatakarda na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres, ya bayyana yaƙin da ake gwabzawa tsakanin Rasha da Ukraine a matsayin wani yanayi na bacin-rai, a dai dai wannan lokaci da yaƙin ya cika watanni 6.

Guterres dai na gabatar da jawabi ne a gaban kwamitin tsaron majalisar da ke birnin New York a ranar Larabar da ta gabata, ya yi amfani da wannan damar domin jinjina wa Turkiya dangane da rawar da ta taka don sake buɗe tashoshin jiragen ruwan Ukraine don ci gaba da raba abinci zuwa sassan duniya.

A cewar Guterres, ziyarar da ya kai ta kasance muhimmiya wajen ba shi damar bin diddigin yarjejeniyar da ta haifar wa ƙasashe masu tasowa da milyoyin mutane kyakkyawan fata, waɗanda kafin nan suke daf da faɗa wa a cikin yanayi na mummunar yunwa.

”Yarjejeniyar ci gaba da fitar da jigilar jiragen ruwa da aka ƙulla a watan yulin da ya gabata na tafiyar kamar yadda ya kamata, domin kuwa jirage na ci gaba da jigilar kayan abinci daga Ukraine zuwa sauran sassa na duniya.”

Sakataren na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce, an yi nasarar cimma yarjejeniyar ne sakamakon kusancin da aka samu tsakanin Ukraine da Rasha saboda ƙoƙarin da gwamnatin Turkiya ta yi.

Yayin ziyarar ta Guterres ya samu damar ziyartar tashar ruwan Odesa da kuma cibiyar da ke tabbatar da cewa an mutunta yarjejeniyar da ke birnin Istanbul.

A cewarsa ana ci gaba da fitar da alkama zuwa sassan duniya daga tashar ruwan Odesa wadda a can baya ta gurgunce, yana mai cewa, yanzu haka tashar ta fara dawo da ayyyukanta sannu a hankali saboda wannan yarjejeniyar.