Wasan mota: Ya yi silar gutsire ƙafar Fatima a Sakkwato

*Tana murnar kammala jarrabawar NECO abin ya faru
*Ba zan taɓa yafe wa Aliyu ba – Fatima
*Ban aikata abinda ake zargi na ba – Aliyu
*Kotu ta tasa ƙeyar matashin zuwa gidan gyara hali
*Ba gudu ba ja da baya wajen ƙwato haƙƙin Fatima – Mahaifan Fatima
*Sai mun tabbatar doka ta yi aiki kan Aliyu, cewar Hukumar Kiyaye Haɗura ta Sakkwato

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Wata ɗalibar matashiya mai suna Fatima Sulaiman Sabo mai shekaru 16 da haihuwa ta rasa ƙafarta a Sakkwato sakamakon yadda ake zargin wani matashi mai suna Aliyu da zama silar gutsire mata ƙafar a lokacin da ya ke wasan tserer da motarsa.

A cewa Fatima, lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan kammala jarrabawar ƙarshe ta kammala sakandare, wato NECO, inda tana zaune, domin jiran mahaifiyarta ta ɗauke ta daga makarantar zuwa gida ibtila’in ya rutsa da ita.

“To bayan kammala jarrabawarmu a Khalifa Intentional Model School, mun ƙare jarrabawa ta ƙarshe ta NECO sai muka fito a cikin makaranta da yake ana wasa da ruwa da komai, amma mu ba ma ciki, ni da wata ƙawata ba ma ciki, to sai wani yaro ya zo yana watsa mana ruwa, sai muka kai shi ƙara.

Mahaifiyar fatima, Malama Hadiza Saleh

Bayan mun kai shi ƙara sai muka fito lokacin bayan an tashi makaranta bayan na kira mamata ta zo ta ɗauke ni. Muna zaune sai wasu maza biyu waɗanda ba ‘yan makarantarmu ba da wasu ɗalibai suka zo suna wasa da motoci, muka je za mu kai su ƙara sai muka ga faransifal ɗin mu ya fito, da ya fito sai ya tsaya bakin makarantar, sai ya ga suna wasa da mota.

“A lokacin ne abin ya faru, da ni da ƙawayena guda uku muna zaune a wurin, to su biyu sun yi ƙoƙarin tashi suka gudu, ni da na tashi guduwa sai na faɗi, shine abin ya faru ta hanyar taka ƙafata,” inji matashiyar da wakilin Manhaja ya zanta da ita a gadonta na asibiti.

A cewar Fatima, “da faruwar lamarin matashin bai yi wata-wata ba ya tsere abinsa, ‘wanda ya ruguza mani rayuwa da nake da burin zama likita nan gaba,” a cewarta.

Duk da faruwar lamarin, a cewar matashiya gwiwowinta ba za su yi sanyi ba wajen ganin burinta ya cika, matuƙar ta samu lafiya, duk da cewa, a zantawa da manema labarai matashiyar ta ce, sam ita ba za ta yafe masa ba kan faruwar lamarin, domin ganganci ne, ba ƙaddara ba.

“Ina kira da gwamnati da hukuma da a taimaka a ƙwato min haƙƙina daga wannan matashin da ya zalunceni,” a ta bakinta.

Malama Hadiza Saleh ce mahaifiyar Fatima. Ta bayyana wa Manhaja cewa za ta yi duk mai yuwa wajen ƙwato haƙƙin ‘yarta Fatima.

“Alhamdulillah, lamarin ya zo da sauƙi kasantuwar akwai faifan bidiyon abinda ya faru na ganganci, saboda yaron nan ya ɗauki motar mahaifansa, ya tafi makarantar da ba tasa ba, ya je yana watsa wa ɗalibai ruwa. Fatima na daga cikin ɗaliban da suka kai ƙara ga malamai cewa, ga abinda yaron nan ke yi na watsa masu ruwa, don ya daina.

“To, wataƙila abin ya vata mashi rai. To, da ma suna wasa da motoci shi da abokansa. Na san wataƙil da zai dawowa ya hange ta ya zo ya taka ƙafarta. Ka ga ganganci ne. Abin haushi, da yin hakan tserewa ya yi.”

Mahaifiyar ta ƙara da cewa, abin ya zo mata  da mamaki kasantuwar tana shirin zuwa ɗaukar yarinyarta, ta samu kira cewa, ta zo Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo da ke Sakkwato ga abinda ke faruwa da ‘yarta.

“Ko da na je wajen na tarar da ƙafar cikin mummunan hali, inda na yi hamdala cewa, abin ya zo da sauƙi bai zama silar rasa rayuwarta ko wani mummunan mataki makamancin haka.

“Don haka a matsiyana na mahaifiyarta ba za mu yafe ba, sai inda qarfinmu ya ƙare, saboda ba yau aka saba samun yaran masu hannu da shuni na wasa da mota suna zama silar rasa rayuka da jikkata mutane da sunan ƙaddara. Don haka matuƙar muka kasance masu bin dokokin Allah waɗannan abubuwan ba za su kasance haka ba, don haka ko dai a cire masa ƙafa shi ma ko kuma a biya diyya,”  inji mahaifiyar Fatima.

Ɗaliba Fatima Sulaiman Sabo tare da Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadurra na Jihar Sakkwato, Yusuf Nadabo

Sai dai a zaman farko da wata Kotun Majistare da ke Sakkwato ta gudanar a ranar Litinin, 22 ga Agusta, 2022, bayan shigar da ƙara da lauyoyin Fatima suka yi, alƙalin kotun ta tasa ƙeyar matashin da ya yi sanadiyyar rasa ƙafar Fatima zuwa gidan gyara halinka har zuwa lokacin da za a cigaba da shari’ar, wato a ranar 29 ga Agustan nan.

Lauyoyin Fatima dai sun shigar da ƙarar ne bisa zargin matashin da tuƙin ganganci, da janyo mummunan rauni, da ma tuƙi ba tare da lasisi ba, wanda ya sava wa sashe na 22 ƙaramin sashe na 10 na dokoki hanya da kuma sashe na 224 na dokokin Jihar Sakkwato na shekarar 2019.

To, amma matashin ya musanta aikatawa bayan karanto masa laifukan da ake zargin sa da aikatawa a gaban kotun.

Duk kuwa da cewa, lauyan mai ƙarar a zaman kotun ya buƙaci kotun da ta duba yiwuwar bayar da belin wanda ake zargin la’akari da tanadin sashe 157 da 161 na dokar laifuka ta Jihar Sakkwato ta 2019 ta hanyar bayar da belin wanda ake zargin har zuwa ƙarshen shari’a, lamarin da lauyan mai ƙara ya bayyana cewa, sam ba su amince da hakan ba, duba da girman laifin da ya aikata kuma akwai yiwuwar matashin ya iya sulalewa daga Nijeriya zuwa ƙasashen ƙetare, a cewar lauyan Fatima.

Sai dai bayan jin ba’asin lauyan mai shigar da ƙara da wanda ake ƙarar, alƙalin kotun ta bayar da umarnin tasa ƙeyar matashin zuwa gidan gyara hali har zuwa 29 ga Agustan nan, domin cigaba da sauraron shari’ar.

Barista Mansur Aliyu shine lauyan wacce ke ƙarar, ya shaida wa Wakilin Blueprint Manhaja cewa, sun shigar da ƙarar ne, domin nema wa Fatima haƙƙinta daga wanda ake zargin.

“An shigar da qarar ne bisa laifukan yin tuqin ganganci da ma tuƙi ba tare da lasisin tuƙi ba. To, da aka shigar da ƙarar an bayar da shi beli a lokacin, saboda wataƙil yana da gata ko shi ɗan manya ne, amma da ƙoƙarin Cif Majistara na babbar kotun da sashen shari’a na CID, an tuhume shi da laifuka, kuma mun ji daɗin da kotu ta kai shi gidan yari,” inji lauyan.

Dr. Sulaiman Boyi Saba shine mahaifin Fatima kuma bayan zaman farko na shari’ar ya bayyana alhininsa kan faruwar lamarin da kuma jin daɗi na tasa qeyar matashin a gidan gyara hali.

“Gaskiya da na samu labarin farko ba aza lamarin ya yi tsanani haka ba, na ɗauka karaya ce, amma da na zo na ga har an cire mata ƙafa na yi baƙin ciki matuƙa.

“Gaskiya na ji daɗi da wannan hukunci na kotu na tsare shi, duba da irin raunin da ya ji wa ‘yata da har ya sanya aka cire mata ƙafa, mun yi murna sosai, don haka fatana a ƙarshen shari’a bai wuce a mana adalci ba, abinda doka ta ce a yi sai a yi na ya biya diyya shi muke buƙata da hukuma ta tabbatar an yi.”

Duk ƙoƙari da muka yi domin jin ta bakin lauyan dake kariyar wanda ake ƙarar kan lamari ya ci tura, domin ya ƙi cewa uffan kan lamarin.

Yaya lamarin Fatima ya ja hankalin al’umma?

Lamarin dai ya ja hankalin al’umma da suke ciki da wajen Jihar Sakkwato bisa la’akari da yadda al’umma da dama ke cigaba da tafka muhawara a shafukan sada zumunta na zamani da ma yadda ƙungiyoyi, hukumomi da ‘yan siyasa ke kai wa Fatima ziyara a gadonta na asibiti.

Daga cikin ƙungiyoyin da suka kai wa Fatima ziyara har da ƙungiyar Fasaudat Support Organization.

Shugabar Gidauniyar Hajiya Fatima Ahmad Maigari tare da sauran jagororin gidauniyar ne suka ziyarci Fatima a Asibitin Koyarwa na Jamiar Usmanu Ɗanfodiyo dake cikin ƙwaryar birnin Sakkwato.

Hajiya Fatima Maigari ta nuna kaɗuwa da halin da Fatima ta sami kanta inda ta ce ta ɗauke shi a matsayin ƙaddara daga Allah, yayin ziyarar dai ta bayar da tallafin kuɗi da wasu kayyaki ga fatima dama gudanar da addu’o’i ga ita Fatimar.

Ita ma dai Uwargidan Gwamnan jihar Sakkwato Hajiya Mariya Aminu Waziri Tambuwal ta kai wa Fatima ziyarar jaje a gadonta na asibti.

Yayin ziyarar Mariya Tambuwal ta tausaya wa Fatima kan Iftila’i da ya sameta, kuma ta ƙarfafe iyayenta da su ci gaba da jinyarta har lokacin da ta samu lafiya tare da saka haƙuri.

To, lokacin da Wakilin Blueprint Manhaja ya ziyarci Fatima a gadonta na asibiti ya ci karo da Kwamandan Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Jihar Sakkwato, Yusuf Nadabo, wanda ya shaida wa Blueprint Manhaja cewa, ya zo asibitin ne bisa umarnin Shugaban Hukumar na Ƙasa, domin jaje ga iyayen Fatima kan lamarin da ya faru da ita, inda ya sha alwashin cewa, tilas su sanya ƙafar wando ɗaya ga ƙananan yara da suke tuqi ba tare da lasisin tuƙi ba.

Fatima a gadon asibiti

“Mun kammala shiri domin soma kamen duk wani yaro dake tuƙi ba tare da lasisi ba yake jin cewa shi ɗan gata ne, za mu kama shi kuma za mu kai shi kotu a hukunta shi,” inji kwamandan.

Kan lamarin Fatima kuwa, kwamandan ya bayyana cewa suna kan tattaunawa da kwamishinan ‘yan sanda, da na shari’a domin tabbatar da cewa doka ta hau kan matashin domin ya zama darasi ga saura.

Duk ƙoƙarin da Wakilin Blueprint Manhaja ya yi na jin ta bakin ɓangaren Aliyu da ake zargin, abun ya ci tura, domin makusantansa da ma lauyoyinsa ba su amince su tattauna da manema labarai ba, amma wata majiya mai tushe a ɓangaren matashin da ta nemi a sakaya sunanta, ta musanta zargin cewa iyayen Aliyu sun yi biris da nuna kulawa da Fatima kamar yadda mahaifiyar Fatima ta zarga.

A cewar majiyar da iyayen Aliyu da faruwar lamarin suka bai wa iyayen Fatima Naira 100,000, domin soma kula da ita, baya ga kai da komowar da suke yi a asibitin.

Sai dai kuma habaici da ma surutan da ake wa ‘yan ɓangaren Aliyu ne ya sanya su ja da baya, don gudun abinda kan iya zuwa ya komo, inji majiyar.