Gwamnatin Bauchi za ta kafa kotuna don ƙwato bashin da aka ba manoman alkama

Spread the love

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Jihar Bauchi za ta kafa wasu kotuna guda uku na musamman, ɗaya a kowace mazaɓar Sanata waɗanda za su riƙa gudanar da shari’o’i na musamman, a cewar shugaban ƙungiyar masu noman rani na alkama na jiha, Mohammed Juli Adamu.

Shugaban ƙungiyar ya bayyana cewar, kafa waɗannan kotuna na musamman ya biyo bayan tattaunawa ne da ƙungiyar tasu ta yi da babban mai shari’a ta Jihar Bauchi, Mai Shari’a Rabi Talatu Umar, yayin da ‘yan ƙungiyar suka kai mata koke-koke kan ƙememe da manoman alkama suke yi na rashin biyan bashin noman alkama.

Adamu, wanda ya yi wannan furuci a garin Bauchi cikin makon nan yayin da yake yin hira da manema labarai, ya bayyana cewar, babbar mai shari’a ta jiha, Mai Shara’a Rabi Talatu Umar ita ce ta yi wa ƙungiyar alƙawarin kafa waɗannan kotuna, bayan da ta saurari koke-koken rashin jituwa da ke faruwa a tsakanin ƙungiyar da masu noman alkama na jihar Bauchi.

Ita dai wannan ƙungiya ta kasance a tsakanin manoma alkama ne da babban bankin tarayyar Nijeriya (CBN) bisa samar da kayayyaki ko kuɗaɗen ayyukan gona a ƙarƙashin shirin aikin noman rani na musamman na Gwamnatin Tarayya mai taken “Anchor Borrowers”.

Alh. Mohammed Adamu ya bayyana cewar, ƙungiyar tana samun ƙalubale daga manoman alkama wajen dawo da basukan kayayyakin noman alkama da suka karɓa a kakar da ta gabata yadda wasu daga cikinsu suke gurfanar da ƙungiyar gaban shari’a kan kada a nemi ƙuntata masu akan biyan bashi.

“A nan qaramar hukumar Bauchi akwai wanda muka ba shi hekta 59 na gona, ya bayar da buhunan alkama guda takwas kaɗai. Da muka yi masa magana sai yaje yayi ƙarar mu a gaban ‘Upper Shari’a Court’ yana roƙon kotu kada a tambaye shi biyan bashin abubuwa da ya karɓa.

“Lauyan ƙungiyar tamu da yake yin bayani akan kayayyakin da wannan manomi ya karɓa waɗanda aka jimlata su akan kuɗi naira miliyan takwas, sai wani mutum da yake zaune a kotun wanda shi ba lauyan kare mai ƙara bane, ya ce wannan magana da yake yin a bayar da shaida ne, ba kariya ba. Daga nan sai Alƙali ya ɗage shara’ar sai bayan wata guda.”

Adamu ya cigaba da bayani: “Ire-iren waɗannan manoma basu da niyya biyan basukan kayayyakin noma da suka karɓa. Wannan shine irin tsarin da waɗannan manoma suke bukata, su je kotu a riƙa ɗaga batun ya nausa cikin lokaci mai tsawo yadda batun zai lalace da haka.”

Shugaba Adamu sai ya bayyana cewar, “wannan kuma gaskiya ba tsari ba ne da shirin Gwamnatin Tarayya da Babban Bankin Tarayya (CBN) na ‘Anchor Borrower’ za su yarda da shi. Shi ne maƙasudin da ya sanya na kira ku ‘yan jarida domin bayyana maku halin da ƙungiya take ciki da ire-iren matakai da za ta ɗauka na gudanar da ayyukanta”.

Adamu ya bayyana cewar, kimanin manoma guda biyar ne a cikin ƙaramar hukumar Bauchi a halin yanzu suka kai ƙungiyar mu a gaban shara’a, kuma babu shakkar ƙaruwar su kamar yadda halayen waɗansu manoman ke nunawa.

Ya kuma bayyana cewar, a noman ranin watan Disamba da ya gabata, ƙungiyar ta raba gonaki kimanin kadada 7, 310 wa manoma fiye da ɗari shida a ɗaukacin cikin Jihar Bauchi.

Ya ce a taron da ƙungiyar ta ƙasa ta yi a garin Kano a ranar 20 ga watan Agusta da ya gabata, an zartar da shawarar cewa, duk manomin da bai samu damar noman alkama ba, kamar yadda ya karɓi bashin kayayyakin noma wa, yana iya biyan bashin da abinda ya noma, walau masara ce ko dawa, ko kuma da kuɗaɗe, kamar yadda hali ya samu.

Shirin noman rani na ‘Anchor Borrowers’ dai dake ƙarƙashin jagorancin babban Bankin Tarayyar Nijeriya ya duƙufa ne da zummar wadatar da ƙasa da abinci, haɗi da samar da kuɗaɗen shigowa na ƙetare (Foreign Reserves) ta hanyar kasuwancin albarkatun da ake nomawa a ƙasashen ƙetare. Bankin CBN dai yana sayen kowane buhun alkama daga wajen manomi akan kuɗi naira dubu talatin da takwas.

By Editor