Ana cigaba da farfaɗo da yankin Xinjiang bayan cimma burin kawar da talauci

Daga CMG HAUSA

An labarta yayin taron watsa labarai game da “Sakamakon da yankin Xinjiang na ƙasar Sin ya samu cikin shekaru goma da suka gabata” a safiyar yau Asabar cewa, gwamnatin yankin Xinjiang tana kara mai da hankali kan aikin da take gudanarwa a ƙauyuka bayan da aka cimma burin kawar da talauci, kuma nan gaba za ta ci gaba da ƙoƙarin farfaɗo da kauyukan yankin daga fannoni biyar wato sana’o’in ƙauyuka, da ƙwararru, da al’adu, da hallitu masu rai da marasa rai da kuma ƙungiyoyin JKS, ta yadda za a cimma burin farfaɗo da ƙauyukan dake faɗin yankin.

A halin da ake ciki, ana aiwatar da tsarin samar da tallafi da sa ido domin hana sake shiga mawuyancin yanayi a faɗin yankin Xinjiang, a sa’i ɗaya, an fitar da manufofin da abin ya shafa domin ci gaba da samar da tallafi ga masu buƙata a fannonin ba da ilmi, da kiwon lafiya, da gidaje da sauransu.

Ya zuwa ƙarshen watan Yulin bana, adadin mutanen da aka fitar da su daga ƙangin talauci wadanda suka samu guraben ayyukan yi a fadin yankin ya kai miliyan 1 da dubu 86, kuma adadin kuɗin shigar kowanne manomin da aka fitar daga ƙangin talauci a yankin, ya kai kuɗin Sin yuan 14,798 a shekarar 2021, adadin da ya karu da kaso 19.55 bisa ɗari idan aka kwatanta shi da na shekarar 2020.

Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa