Xi ya amsa wasiƙar iyalan fursunonin sojojin Birtaniya na jirgin ruwa samfurin “Lisbon Maru”

Daga CMG HAUSA

A kwanakin baya shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya amsa wasiƙar da iyalan fursunonin sojojin Birtaniya da aka kama a jirgin ruwan dakon kaya na “Lisbon Maru” na ƙasar Japan suka aika masa, inda ya bayyana cewa, yana fatan ƙarin abokan Sinawa na Birtaniya, za su ba da gudumowa ga hulɗar dake tsakanin Sin da Birtaniya.

Xi ya bayyana cewa, masuntan tsibirin Zhoushan dake lardin Zhejiang na ƙasar Sin sun ceto fursunonin sojojin Birtaniya da suka faɗa cikin teku daga jirgin ruwan “Lisbon Maru” sakamakon harbin sojojin Amurka, a shekarar 1942, lamarin da ya nuna cewa, ƙasar Sin da Birtaniya sun taba haɗa kai domin yaki da harin murdiya a yaƙin duniya na biyu, kana ya shaida cewa, akwai daɗaɗɗen zumunci a tsakanin al’ummomin ƙasashen biyu.

Xi ya jaddada cewa, a bana ake cika shekaru 50 da kulla hulɗar diplomasiyya tsakanin Sin da Birtaniya, kuma a cikin waɗannan shekaru 50 da suka gabata, an ciyar da hulɗar gaba yadda ya kamata, bisa ƙoƙarin da al’ummomin ƙasashen biyu suka yi.

A watan Oktoban shekarar 1942 ne, jirgin ruwan dakon kaya na “Lisbon Maru” wanda sojojin ƙasar Japan suke amfani da shi domin jigilar fursunoni sojojin Birtaniya sama da 1800 zuwa ƙasarsu, ya tashi daga yankin Hong Kong, amma sai sojojin Amurka suka harbi jirgin a kusa da tsibirin Zhoushan, inda fursunoni 843 suka rasa rayuka, sauran wasu 384 suka tsira, saboda ɗaukin da masuntan tsibirin suka kai musu.

Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa