A bar Wike ya yi duk abinda zai yi – cewar Sule Lamido

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya ce babu wani laifi da aka yi wa Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike kuma a rabu da shi ya yi abinda ya ga dama.

Lamido ya bayyana hakan ne a hirar da ya yi a shirin Politics Today na tashar Channels TV cikin makon nan.

Ya ce Jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP na da kundin tsarin mulki da dokoki kuma zaɓe ake yi don zaven duk wani ɗan takara.

A cewarsa: “Mutane na takarar Kansila; wasu su yi nasara, wasu su faɗi. Hakazalika na shugaban ƙaramar hukuma da Gwamna. Saboda haka mene ne matsalar Wike? A ra’ayina wa ya yi wa Wike laifi?

“An yi zaɓen fidda gwani kuma shi Wike da kansa ya ce zaɓen na gaskiya ne babu maguɗi. Saboda haka mene ne matsalar.”

Lamido ya ce Wike ya daina tunanin ya fi kowa ƙarfi a siyasar jihar Ribas don shine Gwamna.

Ya ce: “Wike mutum ɗaya ne fa. Ban tunanin don kawai gwamna ne yana da ikon komai a Ribas. Mutanen Ribas da PDP na da haƙƙinsu,” inji Lamido.