Za a sanya harshen Sinanci cikin manhajar ilimi a Ghana

Daga CMG HAUSA

Babban daraktan ma’aikatar ilimi ta ƙasar Ghana, Divine Yao Ayidzoe, ya ce nan bada jimawa ba, za sanya Sinanci cikin manhajar ilimi ta ƙasar.

Daraktan ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi yayin wani taron da aka shiriya jiya a cibiyar nazarin harshen Sinanci ta Confiscius dake jami’ar Cape Coast ta Cape Coast, babban birnin yankin tsakiyar Ghana.

Da yake jadadda ƙaruwar muhimmancin koyon harshen Sinanci, baya ga harshen da ƙasar ke amfani da shi a hukumance, daraktan ya ce bisa la’akari da faɗaɗar tattalin arzikin ƙasar Sin zuwa na biyu mafi girma a duniya, haƙiƙa waɗanda suka koyi Sinaci sun yi sa’a matuƙa.

Ya kuma buƙaci ɗalibai su yi amfani da damar wajen koyon Sinaci da al’adun Sinawa, domin shiryawa gaba.

A nasa ɓangaren, Ou Yamei, daraktar cibiyar Confiscius, ta bayana cewa, shirin sanya Sinanci cikin manhajar ilimi ta ƙasar Ghana, ya cancanci yabo matuƙa.

Fassarawar Fa’iza Mustapha