Kwankwaso bai yi mana adalci ba – Shekarau

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon gwamnan Kano kuma Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce babu gaskiya a batutuwan da jagoran Jam’iyyar NNPP kuma ɗan takarar shugaban ƙasa, Rabi’u Musa Kwankwaso ke yi cewa sun shigo jam’iyyarsa a makare.

Sanata Shekarau a wata hira da ya yi da manema labarai bayan taron majalisarsa ta Shura a Kano, ya ce har yanzu suna kan tattaunawa da tuntuɓar juna domin sanar da matsayarsu kan ci gaba da zama a NNPP ko akasin haka.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake raɗe-raɗin cewa Malam Shekarau na gab da sauya sheƙa zuwa PDP.

Sai dai duk da cewa Malam Shekarau bai ambaci ko tabbatar da jam’iyyar da zai koma ba idan ya sauya sheqa, Shekarau ya nuna rashin jin daɗinsa kan hanasu wasu muƙamai da kuma hana magoya-bayansa damar takara a NNPP.

Ya ce taron da suka yi a wannan rana amsa ce ta abin da Kwankwaso ke cewa sun shigo jam’iyyar a makare. Saboda tun kafin su shiga jam’iyyarsa akwai yarjejeniya da aka cimma har kafa kwamiti aka yi.

A makon da ya gabata ne Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya shaida wa ‘yan jaridu cewa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC ta rufe karɓar sunayen ‘yan takara lokacin da ɓangaren Shekarau suka gabatar da buƙatunsu na takara.

Kwankwaso ya ce wannan dalili ne ya sa aka yi musu wasu alƙawarin wasu muƙamai idan sun yi nasara a zaɓen 2023.

Sai dai Malam Ibrahim Shekarau ya ce sun gabatar da buƙatunsu ga Sanata Kwankwaso watanni uku kafin cikar wa’adin da INEC ta bayar na daina karɓar sunayen ‘yan takara.

Ya ce tun a ranar 16 ga watan Mayun 2022, aka kafa kwamitin da aka bai wa wa’adin kwanaki uku su gabatar da rahotonsu amma sai suka shafe wata uku babu labari, duk da ƙoƙarin da ɓangarensa suka rinqa yi domin cimma lokaci.

Malam Shekarau ya ce bayan shi da aka bai wa takara sauran mutane da suka koma NNPP tare babu wanda ya samu wani tikitin.

Shekarau ya ce babu mamaki kwamitin da aka naɗa ƙarƙashin ɗan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar, Abba Kabiru Yusuf, su suka rinƙa jan ƙafa.

A cewarsa har rugawa ya yi Abuja domin tattaunawa da Kwankwaso amma babu wani abin da ya sauya.

Sanata ya jadada cewa akwai kyakyawar alaƙa tsakaninsa da Kwankwaso, babu rashin jituwa ko wata matsala tsakaninsu.
Sai dai duk abin da zai yi dole ya ke duba buƙatun mutanensa.

Sanatan ya ce waɗannan batutuwa su suka sanya majalisarsa ta Shura ke laluben mafita, kuma tuni suke ta samun gayyata daga jam’iyyu daban-daban na ƙasa.

Kuma a cewarsa nan da ‘yan kwanaki kaɗan za su tabbatarwa al’umma matsayarsu.