Daga AMINA YUSUF ALI
Gwamnati jihar Anambra a yanzu haka ta shirya tsaf don yin rusau ga wasu rumfunan kasuwa da ta ce ba a gina su kan ƙa’ida ba.
Ita dai wannan kasuwa ita ce kasuwar sayar da sassan gyaran mota wadda ake fi sani da NASPA da yake a Zone-14 a yankin Nnewi.
Kwamishinan kasuwanci da masana’antu na jihar, Dakta Obinna Ngonadi, shi ya bayyana haka bayan ziyarar gani da ido da ya kai na rangadin kasuwar tare da shugaban hukumar tsara gine-gine na jihar, Mista Chike Maduekwe.
Kwamishinan ya bayyana rashin jin daɗinsa a kan yadda aka wulaqanta rumfunan gwamnati a kasuwar NASPA ta Nnewi, a yayin da kullum ‘yan kasuwar suke qorafin gwamnati ƙa qi ta gina musu rumfuna da ayyukan raya kasuwar tasu.
Ya bayyana takaici ga yadda ofishin sakatariyar kasuwar da gwamnatin jihar ta gina aka mayar da ginin ƙasan benen shaguna waɗanda aka sayar da su ga ɗaiɗaikun mutane.
Sannan ya bayyana takaici da a kan yadda hatta ofishin hukumar kashe gobara da gwamnati ta gina a kasuwar shi ma an mayar da shi shaguna an sayar wa mutane. Yanzu haka saboda cunkushewar wajen ma motar kashe gobarar ba za ta iya ko motsawa ba.
Ngonadi ya kira shugabannin riƙon ƙwarya na kasuwar da masu ruwa da tsakinsu da su cire waɗannan abubuwa don a cire cunkoso a samu hanya.
Sannan ya yi gargaɗin cewa, matuƙar ba su yi biyayya ga wannan umarni ba, gwamnatin jihar za ta rushe kwamitin nasu ta nemo waɗanda za su taimaka wa gwamnati don samar da cigaba a jihar.
Shi kuma Maduekwe ya bayyana cewa, idan har ba su je sun zauna da hukumar tsara gine-gine ba sun samu sahalewarta ba, dukkan haramtattu shagunan da suke a kasuwar ta NASPA, Agbedo United, F-Line da Zone-14 za su fuskanci rusau.