Benzema ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Turai na bana

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ɗan wasan gaban Faransa Karim Benzema ya lashe kyautar gwarzon UEFA na bana, bikin da aka gudanar da shi a Istanbul na ƙasar Tukiyya a jiya Alhamis.

Baya ga Benzema, ɓangaren mata ’yar Spain Alexia Putellas, ce ta lashe kyautar na wannan karo.

Karim Benzema mai shekaru 34, da ke taka leda a Real Madrid ya samun wannan nasara a kan yan wasa da suka haɗa Thibaut Courtois da ke ƙungiyar ta Real Madrid da kuma ɗan ƙasar Belgium daga Manchester City Kevin de Bruyne.

Karim Benzema ya zura ƙwallaye 44 a wasanni 46 da ya yi da Real, banda hakan, ɗan wasan ya yi nasara a gasar zakarun Turai tare da ƙungiyar Faransa.

Yanzu kam Benzema ya kama hanyar lashe kytautar Ballon D’or na farko kamar dai yadda hasashe ya nuna a yayin bikin da za a yi ranar 17 ga Oktoba a birnin Paris na ƙasar Faransa.

Tsohon ɗan wasan ƙungiyar Lyon, Karim Benzema ya zama ɗan wasan Faransa na biyu da ya samu wannan kyautar daga hukumar ƙwallon ƙafar Turai, bayan Franck Ribery da ya lashe wannan kyauta a 2013.

Kafin shi, ’yan wasan Real Madrid biyu ne suka taɓa lashe wannan kyauta: Wato Cristiano Ronaldo a shekarun 2014, 2016, 2017 da Luka Modric a shekarar 2018.