CMG ra watsa shagalin murnar bikin tsakar yanayin kaka ta shekarar 2022

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Bikin tsakar yanayin kaka yana ɗaya daga cikin manyan bakukuwan gargajiya na ƙasar Sin.

A wannan rana, Sinawa su kan haɗu, tare da kallon duniyar wata, da cin wainar wata, da tunawa da sauran ‘yan uwa tare da yi wa juna fatan alheri.

A daren ranar 10 ga watan Satumba, wato ranar bikin tsakar yanayin kaka bisa kalandar gargajiyar ƙasar Sin, babban gidan rediyo da telebijin na ƙasar Sin wato CMG ya watsa shagalin murnar bikin na shekarar 2022, inda aka nuna shirye-shirye masu nishaɗantarwa ga masu kallo na sassan duniya.

Taken shagalin murnar bikin tsakar yanayin kaka na bana shi ne, al’adun duniyar wata, inda shagalin ya nuna al’adun bikin tsakar yanayin kaka da tunanin gida da kuma haɗuwar iyalai ta hanyoyin shirye-shiryen kiɗe-kiɗe da waƙe-waƙe da raye-raye.

Ta hakan, masu kallo za su iya gano al’adun bikin da ƙaunar da Sinawa ke yi masa.

A bana, kafofin watsa labaru na ƙasashen waje da dama ciki har da na Amurka, da Canada, da ƙasashen Turai, da Japan, da Kenya da sauransu, sun watsa shirye-shiryen shagalin da CMG ya gabatar.

A bikin na bana, ‘yan saman jannati dake kumbon Shenzhou-14 Chen Dong, da Liu Yang, da Cai Xuzhe sun yi murnar bikin, wanda shi ne karo na farko da Sinawa suka yi murnar bikin a sararin samaniya.

‘Yan saman jannati uku sun ɗauki bidiyo don yi wa dukkan Sinawa a sassan duniya fatan alheri.

Mai fassara: Zainab Zhang

By Editor