Lewandowsk na iya zama warakar Barcelona – Masu sharhi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Masu sharhi a fagen wasan ƙwallon ƙafa sun bayyana cewa, bayan wani yanayi na firgici da Barcelona ta shiga a kakar da ta gabata, sakamakon fitar wasu daga cikin manyan ’yan wasanta, za a iya cewa yanzu Barcelona ta samo warakar matsalarta.

Fitar babban ɗan wasanta Lionel Messi ya jefa ƙungiyar cikin laluɓen wanda zai maye wagegen giɓin da ya bari.

Kodayake, a watan Fabirairu da ya gabata ta sayo ɗan wasan gaban Gabon Pierre-Emerick Aubameyang wanda kuma ya taka rawar ganinsa wajen ganin ya ceto ƙungiyar daga halin da ya same ta.

Ta kuma ƙara sayen ‘yan wasa da dama ciki har da Robert Lewandowski wanda ta ɗauka daga Beyern Munich, wanda ake gani zai iya zama waraka ga ƙungiyar.

Ko a ranar Laraba da ƙungiyar ta buga wasanta na farko da Viktoria Plzen sai da ɗan wasan ya ci ƙwallo uku karon farko tun dawowarsa ƙungiyar.

Ɗan wasan mai shekara 34 ɗan ƙasar Poland ya nuna kimar da ya ke da ita a ƙungiyar inda ya ci ƙwallo takwas cikin wasa biyar da ya buga bayan barinsa Bayern a watan Yuli.

Lewandowski, wanda ya taimaka wa Bayern ta lashe gasar 2019-20, ya fara buga wasansa na farko a Barcelona a gasar zakarun nahiyar Turai da ƙafar dama.

Da waɗannan ƙwallaye magoya bayan Barcelona sun fara jin cewa ɗan wasan zai iya zama warakar matsalar da suka faɗa tun bayan rabuwa da Messi.

Sai dai wasu na ganin shekaru za su iya zama koma baya ga ɗan wasan a wannan lokaci.