Kamfanin Fulawa Mai Kwabo ya sake rabon motoci don ƙarfafa gwiwar abokan hulɗa

Daga AMINA YUSUF ALI

A wani yunƙuri na ƙara ƙarfafa kyakkyawar alaƙarsu da masu ruwa da tsaki a kasuwancinsu, kamfanin Fulawa Mai Kwabo (Flour Mills of Nigerai, FMN), Kamfanin da ya yi zarra a Nijeriya wajen samar da kaya masu inganci kuma mamallakin sanannen kamfanin kayan abincin nan na Golden Penny, ya ba da kyautar tireloli ga dilolinsu da suka cancanta a ƙarƙashin tsarin  B2B.

Kamfanin ya yi rabon ne domin ƙara danƙon alaƙar dake tsakaninsa da dilolin da kuma ƙara sauƙasƙa musu harkokin tafiyar da kasuwancinsu. 

Ranar da  aka gabatar da taron, kamfanin ya rarraba sabbin tireloli dal, guda 22 masu ɗaukar tan 20 a shalkwatar kamfanin Golden Penny dake Apapa, a jihar Legas. 

Mutane  22 da suka samu kyaututtukan su ne dilolin fulawar biredi waɗanda suka nuna jajircewarsu a kan aiki shekarar da ta gabata. 

Manajan daraktan FMN na ɓangaren kayan abinci Mista Delvin Hainsworth ya bayyana cewa, “tabbatar da kyakkyawar alaƙa tsakaninmu da abokan kasuwancinmu yana ɗaya daga cikin manyan ginshiƙanmu na gina kasuwanci da kuma samar da abinci ga al’ummar ƙasar nan”. A don haka a cewar sa, kyaututtukan da aka raba a yau za su ƙara taimaka wa dilolinsu don tabbatar da kayan abincin sun isa ga al’umma.  

Ɗaya daga cikin waɗanda suka samu tagomashin sabuwar tirela, Badejo M Adegboyega, Manajan amfanin Felicia Modupeoluwa Trading Company Ltd ya bayyana godiyarsa ga kamfanin FMN. Sannan ya ƙara da cewa, yana matuƙar jin daɗin harka da kamfanin a tsahon shekaru 32 da suka yi suna harka tare.   

Shi dai kamfanin FMN shi ne ma fi girman kamfanin da yake samar da abinci da kuma kayan Noma tun a shekarar 1960. Kuma yana da rassa a jihohi 12 a faɗin Nijeriya.