2023: Ba za mu sake saka makusantan ‘yan takara a tawagar yaƙin neman zaɓen PDP ba – Gwamna Bala

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na Jihar Bauchi ya bayyana cewar tawagar yaqin neman zaɓe na Jam’iyyar PDP ya zuwa zaɓen shekarar 2023 ba za ta ƙunshi jinsin ‘yan uwa ko dangin ɗan takara domin ƙarfafa su ta hanyar siyasa ba.

Sanata Bala ya ce jam’iyyar ta PDP ba za ta ƙara amincewa ta faɗa cikin wancan kuskure da makamancinsa ya faru a shekara ta 2019 ba, lokacin da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubar ya ɗora makusantansa akan tawagar yaƙin neman zaɓe, da hakan ya yi sanadiyyar faɗuwarsa a wancan zave ba.

Idan za a iya tunawa dai Atiku Abubakar a zaɓen shekara ta 2019 ya tsunduma makusan tansa cikin tawagar yaƙin neman zaɓensa, da suka ɗauka an yi hakan ne domin ƙarfafa su, lamarin da ya cusa sakaci a cikin yaƙin neman zaɓen, ya kuma haddasa faɗuwar Atiku a zaɓen.

“Ba za mu amince wani shugaban jam’iyya ko ɗan takara ya cusa mana ‘yan uwa ko danginsa a cikin tawagar yaƙin neman zaɓe ba domin su samu tagomashin ƙarfafa kansu. Makamancin hakan ya faru Atiku Abubakar a zaɓen shekara ta 2019 lokacin da ya cusa makusantansa a cikin tawagar yaƙin neman zaɓe, lamarin da ya sanya ba a taɓuka komai ba, kuma wannan sakacin ya sanya Atiku ya faɗi a zaɓe. Ba za mu maimaita wancan kuskure ba.”

Gwamna, wanda a ranar satin da ya gabata ne yake yin wannan jawabi yayin buɗe taron masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar PDP a Jihar Bauchi, sai kuma ya ce, “saboda haka duk wanda ya haska ya yi hakan na ba tare da alaƙar dangantaka ba, face ɗan jam’iyya da ya yi fice cikin tsararraki.”

Gwamnan ya kuma bayyana cewar, “haka muke zalla daga sama zuwa ƙasa, muna yin ladabi da girmama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyarmu, kuma muna tare da shi, muna girmama shugabancin jam’iyyar mu a matakin ƙasa da ‘yan kwamitin gudanawarta, haɗi da shugabancin jiha na jam’iyyar. Ina buƙatar tsari bai ɗaya ne na neman takarancin shugabancin ƙasa, na gwamna da kowane matakin takara na jam’iyyar mu ta PDP, kuma haka za mu tafi bai ɗaya.”

Sanata Bala Mohammed wanda ya nuna buƙatar duk wani badakaren ɗan siyasa ya kasance mai biyayya ga ƙa’idojin jam’iyyarsa, ya ce,“mun yi dubi wa ƙa’idojin jam’iyya, da tsarin da ya dace mu bi. bada jimawa ba za a kaɗa gangar yaƙin takarar neman zaɓe, kuma za mu karaɗe ko’ina, wace irin tawagar yaƙin neman zaɓe ne ya kamata mu samar?