2023: Al’ummar Tibi sun bayyana goyon bayansu ga Gwamna Sule a karo na biyu

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Al’ummar ƙabilar Tibi na ƙasa reshen Jihar Nasarawa sun bayyana tare da tabbatar wa gwamnan jihar, Injiniya Abdullahi Sule cikakken goyon bayansu.

Shugabannin al’ummar Tibin sun bayyana haka ne a lokacin da suka jagoranci ɗimbin al’ummarsu inda suka ziyarci gwamnan a gidan gwamnati dake Lafiya babban birnin jihar.

A jawabin shugaban ‘yan ƙabilar Tibin reshen jihar Nasarawa, Kwamared Peter Ahemba ya ce babban dalilin sake mara wa gwamnan baya don tabbatar da nasarar sa karo na 2 shine yadda gwamnatinsa ta shawo kan matsalar rashin tsaro da ya addabi jihar da daɗewa.

A cewarsa hawan gwamnan mulki ke da wuya sai ya fara yin duka mai yuwa wajen tabbatar al’ummar su na Tibin dake gudun hijira a wasu garuruwa sun dawo muhallinsu na ainihi.

Ya ce ba shakka matakin yana haifar da ɗa mai ido sa’anan ya bai wa ɗimbin al’ummarsu damar dawowa da cigaba da gudanar da rayuwarsu.

Kwamared Peter Ahemba ya cigaba da bayyana cewa, “a yanzu al’ummominmu suna kwanciya da idanunsu biyu a rufe a ƙauyukansu suna kuma gudanar da harkokin noman su yadda suka saba savanin yadda lamarin ya kasance a da. Shi ya sa har ila yau aka samu ingantacce da kuma wadatattun amfanin gona a bana a faɗin jihar nan baki ɗaya.

Saboda haka bamu da wani zaɓi illa mu nuna cikakken goyon bayan mu ga gwamnan musamman ta fito kwan mu da ƙwarƙwata mu sake zaɓen shi karo na 2 a matsayin gwamnan jihar nan mai cikakken iko,” inji shi.

A nasa ɓangaren da yake maida martanin jawabi Gwamnan Jihar Injiniya Abdullahi Sule ya gode wa al’ummar Tibi da suka fito su da iyalan su baki ɗaya duk da ana ruwan sama inda suka ziyarce shi tare da tabbatar masa da goyon bayan.

Ya ce wannan shine ziyara ta farko da ya haɗo kawunan shugabannin al’ummar jihar da ƙasa baki ɗaya ba tare da nuna bambancin addini ko ƙabilanci ba inda ya buƙace su su cigaba da haɗa kai don su cigaba da amfana da kyawawan shirye-shiryen gwamnatinsa.

Gwamnan daga nan sai ya kuma yi amfani da damar inda ya sanar musu cewa nan ba da daɗewa ba gwamnatinsa za ta kafa masarautar Tibaben a jihar ta kuma ƙara yawan al’ummarsu a cikin gwamnatinsa da sauransu inda ya kuma ba su kyautar mota don gudanar da harkokin su na yau da kullum.