Daga CMG HAUSA
Tarayyar Najeniya, babbar kasuwa ce da ƙasar Sin take zuba jari, da gudanar da cinikayya, da fitar da kayayyaki, da kuma ayyukan gine-gine a nahiyar Afirka.
Kwanan baya ministan masana’antu da cinikayya da zuba jari na tarayyar Najeriya Otunba Adebayo ya bayyana yayin da ya zanta da wakilin CMG cewa, Najeriya da Sin suna gudanar da hadin gwiwar ƙut-da-ƙut a fannonin gina manyan kayayyakin more rayuwar al’umma da tattalin arziki da cinikayya, kuma Najeriya tana maraba da kamfanonin ƙasar Sin da su zuba jari tare kuma da kafa kamfanoni a ƙasar, kana tana fatan za ta yi amfani da damar shiga bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa daga ƙetare na ƙasa da ƙasa na ƙasar Sin karo na 5 da za a shirya a bana, domin tallata kayayyakin Najeriya ga masu sayayya na ƙasar Sin.
Rahotanni sun nuna cewa, gaba ɗaya jimillar darajar cinikayyar dake tsakanin ƙasar Sin da tarayyar Najeriya a shekarar 2021, ta kai dalar Amurka biliyan 25.68, adadin da ya ƙaru da kaso 33.3 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara.
Game da halin da ake ciki a ɓangaren hadin gwiwar dake tsakanin Najeriya da Sin a fannonin gina manyan kayayyakin more rayuwar al’umma da tattalin arziki da cinikayya da zuba jari kuwa, minista Adebayo yana mai cewa, tun bayan da aka kulla hulɗar diplomasiyya tsakanin ƙasashen biyu a shekarar 1971, dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin sassan biyu ta bunƙasa daga dukkan fannoni, kuma nan gaba ana sa ran za a ciyar da haɗin gwiwar dake tsakanin Najeriya da Sin zuwa wani sabon matsayi.
Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa
